Skip to main content

Posts

Showing posts from October, 2021

Ganduje ya bai wa makaho aiki saboda bajintarsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bai wa Ɗahuru Abdulhamid Idris wanda makaho ne, aikin koyarwa a gwamnatin jihar. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Sakataren Labarai na gwamnatin jihar, Abba Anwar ya fitar a ranar Lahadi. Kafin wannan lokaci, Ɗahuru ya kasance yana aikin koyarwa na sa-kai ba tare da ana biyansa wani albashi ba. Sanarwar ta ce bayan da Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Muhammadu Sanusi Kiru, ya jagoranci Ɗahuru zuwa gaban Ganduje ne, a nan Ganduje ya bada umarnin a ɗauke shi aiki sannan a tura shi Makarantar Nakasassu da ke Tudun Maliki don ya ci gaba koyarwa. Yayin ganawar tasu, Ganduje ya yaba wa ƙoƙarin Ɗahuru musamman ma ganin yadda bai bari lalurar makanta ta hana shi bada tasa gudunmawa ga cigaban fannin ilimin jihar ba. Bisa wannan dalili ne Gwamna Ganduje ya ce, “Lallai ka taki matakin da ya dace a rayuwarka. Gwamnatin jihar Kano ta ba ka aikin koyarwa. Kuma na umarci Kwamishinan Ilimi da a tura ka zu

Trump zai kirkiro da manhajar Intanet kamar Facebook

Tsohon shugaban kasar Amurka Donal Trump zai bude shafin Intanet mai kama da Facebook da ya radawa suna Gaskiya da Gaskiya Rahoto: Comrade Musa Garba Augie. Donald Trump ya sanar da shirin kaddamar da wani sabon shafin sada zumunta. Shafin wanda zai sanya wa suna Gaskiya da Gaskiya, zai kasance karkashin gudanarwar wata kungiyar da ke kula da harkokin kimiyya da fasaha a tafiyarsa ta siyasa. Tsohon shugaban ya ce zai kirkikiri kamfanin ne da fatan jama'a za su yi abun da ya kira zaluncin manyan kamfanonin fasaha, irinsu Facebook da Twitter bara'a. Ana sa ran Shafin Gaskiya da Gaskiya na Mista Trump, zai fara aiki a watan Nuwamba tare da wasu kayyadaddun mutane da za su fara amfani da shi a matsayin gwaji, kafin daga baya ya zama na kowa da kowa. A baya dai shafukan Facebook da na Twitter suka rufe shafin tsohon shugaban Amurkan saboda harin da magoya bayansa suka kai wa majalisar kasar.

Najeriya ta ce ita mamba ce ta Majalisar Ɗinkin Duniya wadda take da dokoki na kare duk wani mutum da ba shi da fasfo na wata ƙasa,

Najeriya ta ce ita mamba ce ta Majalisar Ɗinkin Duniya wadda take da dokoki na kare duk wani mutum da ba shi da fasfo na wata ƙasa, wanda a kan haka ta ƙi amsa buƙatar shugaban Turkiyya ta korar wasu ƴan ƙasarsa. Rahoto: Comrade Musa Garba Augie. Fadar Shugaban Najeriya ta yi bayani kan dalilan da suka sa gwamnatin kasar ta ƙi amincewa da bukatar shugaban Turkiyya Racib Tayyeb Erdogan na ba shi hadin kai wajen daukar mataki kan magoya bayan Fathullah Gullen da ƙadarorinsa da ke Najeriya. Shugaba Recep Tayyip Erdoğan na Turkiyya ya ce wadanda suka shirya yi masa juyin mulki a 2016 suna nan har yanzu a Najeriya suna gudanar da harkokinsu inda ya nemi hadin kan Najeriya wajen murkushe su. Erdogan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin ziyararsa ta kwana biyu a Najeriya, inda suka tattauna kan batutuwa da yawa na alaƙa tsakaninsa da Shugaba Buhari. Sai dai ba wannan ne karo na farko da Turkiyya take neman wannan buƙatar ba, ta sha neman hakan ta wajen jakadanta da ke Najeriya

Gwamnatin Kaduna ta ce an kashe mutum 343 cikin wata uku a jihar

Daga: Comrade Musa Garba Augie. Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum 343 sakamakon ayyukan 'yan fashin daji da sauran tashe-tashen hankali cikin wata uku. Cikin wani rahoto da ya fitar ranar Laraba, Kwamashinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa 'yan bindigar da ake zaton 'yan fashin daji ne sun sace mutum 830 a watannin. Rahoton ya duba rikice-rikicen da suka faru ne daga 1 ga watan Yuli zuwa 30 ga Satumban 2021. Sai dai rahoton ya nuna cewa adadin waɗanda aka sace a wata ukun ya ƙaru a kan na watannin Afrilu zuwa Yuni, inda aka sace 774 kuma aka kashe 222. •Na cire ɗana daga makarantar gwamnati saboda 'yan fashi na ƙoƙarin sace shi - El-Rufai •'Yan bindiga sun kai hari Makarantar Sojoji ta NDA •Abin da ya sa El-Rufai ba ya goyon bayan yin sulhu da ƴan bindiga •A gefe guda kuma, Mista Aruwan ya ce jami'an tsaro sun kashe jumillar 'yan fashi 69 a wurare daba-daban na jihar tare da tarwatsa sansanon

Kotu ta umarci kakakin majalisar Kano da wasu mutane 5 su gurfana a gabanta

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar Laraba, ta umarci kakakin majalisar jihar Kano da wasu mutane biyar su gurfana a gabanta.  Wannan umurnin ya biyo bayan wata takarda da aka shigar ta tsohon Shugaban Korafe-korafen Jama'a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa na Jihar Kano, Muhyi Rimin-Gado wanda gwamnatin Kano ta dakatar a watannin baya.  Sauran wadanda ake kara sun hada da Kwamishinan Shari'a na Kano, Babban Akantan jihar Kano, Kwamishinan 'yan sanda na Kano da Sufeto Janar na' yan sanda.  Mai shari’a Jane Inyang, wacce ta ba da umarnin, ta nemi su kawo dalili cikin kwanaki biyar da zai sa kotu ba za tayi abinda wanda ya gabatar da ƙara ya nema ba.  Inyang ta bada umarnin a sanar da wadanda ake kara a cikin kwanaki biyar sannan ta dage karar zuwa ranar 3 ga Nuwamba, don cigaba da sauraron karar.  Tun da farko, mai gabatar da kara Rimin-Gado a cikin karar ta bakin lauyansa Barista Muhammad Dan’azumi ya gabatar, ya nemi a hana mutane shida da ake kara b

A karon farko an bi umarnin IPOB na zama a gida a Abia Ikpeazu

Manyan tituna sun zama wayam, sannan shaguna da ma'aikatun gwamnati sun kasance a rufe a fadin Umuahia babban birnin jihar Abia da ke kudancin Najeriya, sakamakon kullen da kungiyar 'yan awaren Biafra ta IPOB ta saka. Ko a baya IPOB ta saka irin wannan doka ta zama a gida, da ya hada da rufe makarantu da kasuwanni amma ba ta yi tasiri ba. A Litinin din da ta gabata mazauna birnin Umuahia sun ce mambobin IPOB sun rika yawo da bindigogi kan tituna, suna hantarar mutane su shige gidajensu. To sai dai mazauna babban birnin jahar ta Abia sun sami kansu cikin tsaka mai wuya, bayan da gwamnatin jahar ta yi gargaɗin cewa duk ma'aikacin da bai fito aiki ba zai fuskanci hukunci. To amma bayanai daga jaridar Daily Trust sun nuna cewa kashi 80 basu fita aiki ba a yau Litinin.

Wasu jigajigai a jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC a jihar Yobe

Mataimakin shugaban PDP da wasu manyan shugabanni sun sauya sheƙa zuwa Jam'iyyar APC a jihar Yobe dake Arewa maso gabashin Nigeria. Mataimakin shugaban PDP reshen jihar Yobe, tare da wasu manyan jiga-jigai sun koma jam'iyyar APC mai mulki A cewar waɗanda suka sauya shekan, ba bu wani dalili da zai sa su cigaba da zama cikin PDP, saboda shugaban ƙasa na bukatar goyon baya Gwamna Mai Mala Buni, na jihar Yobe, ya tabbatar musu da cewa ba za'a nuna musu banbanci ba. Wasu daga cikin shugabannin jam'iyyar hammaya PDP reshen jihar Yobe, tare da mambobi sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki. Vanguard ta rahoto cewa daga cikin waɗanda suka koma APC har da, mataimakin shugaban PDP na jiha, Alhaji Usman Amale, da mataimakin sakatare, Malam Ahmadu Biriri. Jaridar Illela Daily Post ta ruwaito cewa gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, shine ya karbi masu sauya shekan ranar Talata a Damaturu. Gwamna Mai Mala Buni, wanda shine shugaban kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙas

Kamfanin Facebook Zai Canza Sunan Sa.

LABARU DA DUMI-DUMIN SU! Shahararren dandalin sada zumunta na Facebook Inc yana shirin sake sunan kansa da sabon suna a mako mai zuwa, shafin yanar gizo na fasahar Amurka Verge ya ruwaito a ranar Talata, inda ya ambaci wata majiya da ke da masaniya kai tsaye kan lamarin.  Babban Jami'i kuma Shugaban Facebook Mark Zuckerberg yana shirin yin magana game da canjin sunan a taron haɗin gwiwa na kamfani na shekara -shekara a ranar 28 ga Oktoba, amma ana iya bayyana shi da wuri, inji rahoton Verge. Labarin na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin ke fuskantar karuwar sanya ido daga gwamnati a Amurka kan harkokin kasuwancinsa.  Sake canza sunan zai sanya aikace -aikacen kafofin watsa labarun Facebook a matsayin ɗayan samfura da yawa a ƙarƙashin kamfanin, wanda kuma zai kula da sauran manhajojin sa kamar Instagram, WhatsApp, Oculus da sauran su, in ji rahoton Verge.  Ba sabon abu bane a Silicon Valley don kamfanoni sun canza sunayensu yayin da suke neman fadada ayyukan su. Google

Allah ya yi wa jikar Ahmadu Bello Sardauna ta farko rasuwa

Allah ya yi wa Hajiya Hadiza Shehu Kangiwa, jikar Sardauna ta farko rasuwa Marigayiyan ta rasu ne tana da shekaru 61 a duniya kuma ta bar 'ya'ya guda uku An yi mata sallar jana'iza a gidan Sardauna da ke Diori Hammani road a Sokoto Jikar tsohon Firimiyan tsohuwar Yankin Arewacin Nigeria, Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto ta riga mu gidan gaskiya. Hajiya Hadiza ta rasu ne a Sokoto bayan fama da fajeruwar rashin lafiya kamar yadda ya Illela Daily Post ta samu labari. Marigayiyar diyar Wamban Kano ne, Abubakar Dan Maje. Hajiya Hadiza ta auri tsohon gwamnan tsohuwar jihar Sokoto, Shehu Kangiwa. An haife ta ne a shekarar 1960, shekarar da Najeriya ta samu 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya. Ta rasu ta bar 'ya'ya uku kuma an yi mata sallar jana'iza a gidan marigayi firimiyan arewa da ke Diori Hammani road a Sokoto. Yar Tafawa Balewa ta tabbatar da rasuwar Hajiya Hadiza Jaridar Neptune Prime ta ruwaito cewar kawarta, Hajiya Binta Tafa

Musulmai Sun Yi Martani Ga Gumi Bayan Sukar Da Yayi Akan Maulud

Musulman Najeriya sun mamaye shafin Facebook na Dr. Ahmad Gumi. shahararren mai fafutukar kare hakkin ‘yan fashin daji bayan yayi suka ga maulidi a shafin a daidai lokacin da musulman suke  tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad SAWA.  A kowace shekara a cikin watan Rabi’ul Awwal, Musulmin duniya suna tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad ta hanyar karanta Alƙur’ani mai girma, ƙasidun yabo ya Annabi da karanta tarihin rayuwar sa. Shafin Dr. Gumi na Facebook ya samu sharhi sama da 600 har zuwa lokacin nan a tare da cewa suka yayi akan maulidin, amma da yawan su suna rubuta "Happy Maulud,"  duk da sun karanta sukar da yayi.   Karantarwar Dr Gumi tana fuskantar tsaiko da rashin tasiri akan mutane bayan ya karkatar da hankalin sa daga taimakon waɗanda rikicin yan fashin daji ya rutsa da su a arewa maso yammacin Najeriya zuwa neman haƙƙin masu aikata laifin.

Wataƙila nan da shekara kuma ku fara hawa tasi mai tashi sama

Business reporter Wani rahoto ya yi hasashen cewa daga nan zuwa shakerar 2040 za a samar da irin wannan mota guda 430,000 a faɗin duniya. Da zarar aka yi batun tasi mai tashi sama don kai mutane anguwa a cikin gari, abin da ke fara zuwa zukatan wasu shi ne sanannen fim dinnan na zane wato 'The Jetsons'. Cartoon din wanda aka yi a shekarar 1960 ya nuna wasu iyalai da ke rayuwa a wani gari na zamani, inda mutane ke zuwa aiki cikin wasu motoci da ke tashi sama. Shekaru 20 a karni na 21, wasu masana kimiyya na kokarin mayar da mafarkin waɗanda suka shirya cartoon din Jetsons gaske. A yanzu kamfanonin Uber da Boeing sun samar da motoci masu tashi sama. Wani rahoto ma ya yi hasashen cewa daga nan zuwa shekarar 2040 za a samar da irin wadannan motoci guda 430,000 a faɗin duniya. Wannan kuma na zuwa a dai dai lokacin da ake ci gaba da samar da jirage marasa matuki, da ake hasashen kasuwar su za ta bunkasa da fam biliyan hudu daga nan zuwa 2028. To amma kafin a s

"Annabi Ne Ya Fara Maulidi, Saboda Haka Ba Bidi'a Ba Ne" ~Sheikh Halliru Mataya

FILIN FAHIMTA FUSKA: Sheikh Maraya ya ce annabi ne ya fara yin nuni ga murnar ranar haihuwarsa Sheikh Halliru Maraya, malamin addini a Kaduna ya ce Annabi Muhammad SAW ne ya fara yin nuni ga murnar ranar haihuwarsa da ake kira Maulidi. "An tambayi Annabi Muhammad SAW dangane da azumin Litinin da ya ke yi. Sai annabin ya ce ranar ne aka haife ni", in ji Sheikh Halliru. Malamin ya kara da cewa kamata ya yi Musulmi su girmama watan na Maulidi kasancewar a watan ne Allah ubangiji ya bai wa duniya kyautar da babu irinta ga. duniya wato haihuwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Abubuwan da ya kamata a yi lokacin Maulidi: Malamin ya lissafa wasu. abubuwan da ya kamata a yi a lokacin Maulidi amma wadanda ba su saba da shari'a ba. Sai dai malamin ya ce bai kamata a yi duk abin da shari'a ba ta amince da shi ba kamar cakuɗuwar maza da mata, ihuce-ihuce, shaye-shaye da dai sauransu. Rabi'ul Awwal, wata ne na kalandar musulunci da wani ɓangaren

Buhari ya fusata da kisar gillar da aka yi wa masu cin kasuwa a garin Goronyo dake gabashin jihar Sokoto.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi matukar fusata da kisan gillar da aka yi wa masu cin Kasuwa a Goronyo, Jihar Sokoto inda ya aika wa ƴan bindiga sakon ‘Ta su ta kare’ ranar Litinin. Kakakin fadar shugaban ƙasa, Garba Shehu a wata takarda daga fadar shugaba Buhari ranar Litinin ya bayyana cewa shugaban Buhari ya fusata matuka da kisan da aka yi wa ƴan kasuwa da basu ji ba basu gani ba a kasuwar goronyo. Buhari ya ce wannan karon ƴan bindigan sun kai gwamnati maƙura kuma sun siya da kuɗin su domin sai sun gwammace kiɗa da karatu nan ba da daɗewa ba. ” Ko a yanzu ba su ji da daɗi daga dakarun Najeriya ta sama da kasa ba. Hakan yasa suke bin mutanen da basu ji ba basu gani suna kashe su. Wannan abu ya kai mu makura yanzu kuma lallai su kwana da shirin ta su ta kare. Harin Goronyo A kasuwar Goronyo jihar Sokoto dake ci mako-mako ne ‘yan bindiga suka buda wa mutane wuta inda suka kashe mutum sama da 30 sannan da dama sun ji rauni. Wannan hari ya auku ne kwanaki 12 da wasu ‘ya

Harin Goronyo: 'Yadda muka riƙa kutsawa gidajen matan aure don tsira '

Ƴan uwa da abokar arziƙin mutanen nan 30 zuwa 60 da suka gamu da ajalinsu yayin wani harin ƴan fashin daji a garin Goronyo da ke jihar Sokoto na ci gaba da jimamin rashin ƴan uwan na su. Kamar yadda mane labarai suka tattauna da wasu mazauna garin, inda suka bayyana halin da suka shiga, a lokacin da mahran suka yi wa garin kofar rago tare da buɗe wuta kan mai uwa da wabi. Wani mutum da muka sakaye sunansa, ya ce bai taba ganin tashin hankali a rayuwarsa irin wannan ba, domin ta kai hatta katangar gidan da yake tana jijjiga saboda yadda harbi ya karade gari ko ta ina. "Ina zaune tare da mutane kawai sai muka ji ana barin wuta, aka ce ai ɓarayi ne, karfe 4:30 na maraice, daga nan kuma muka tashi muka ruga da gudu, muka tsallake katanga muka fada wani gida, ko ina barin wuta ake, ba su tafi ba sai ƙarfe shidda, sannan suka hau baburansu suka wuce. A cewar wannan mutumin, Allah ne kawai bai sa kwanansa ya ƙare ba, amma ba don haka ba da tuni shi ma yana cikin mutanen da suka mutu. 

HOTON SARKIN BUNGUDU BAYAN ALLAH YA KUBUTAR DA SHI.

Ga hoton Sarkin Bungudu (Sarkin Yanka Mai Daraja Ta Daya) nan ya na ta yawo a kafafen sadar da zumunta, bayan da Allah Ya kubutar da shi daga hannun masu garkuwa da mutane, wanda ya shafe tsawon kwanaki talatin da biyu (32) a hannunsu. (1) Abu ne mai matukar tayar da hankali, a ce wadannan mutane har suna da karfin halin iya kama Sarki Mai Martaba ta daya, har suna da karfin ikon iya rike Sarki mai martaba ta daya tsawon lokaci, an kuma kasa bibiyarsu a amso shi. (2) Wasu kafafun watsa labarai sun bayyana cewa ba a sako Sarkin Bungudu ba sai da aka biya kudin fansa kimanin naira miliyan ashirin (20,000,000) lakadan ba ajalan ba. (Vision FM, Farin Wata TV). (3) Don Allah ku duba yanayin da Mai Martaba Sarki ya samu kansa a ciki, ku yi la'akari da yadda ya fita daga hayyacinsa!!! Duba hotunan nan nasa da ya ke cikin kayan alfarma na sarauta da kasaita, sannan ka duba hoton da aka dauka bayan samun kubutarsa. A gaskiya dukkan wani nau'i na tashin hankali da

Sokoto: 'Ƴan bindiga sun kashe mutum 49 a kasuwar Goronyo'

Tambuwal Rahotanni daga jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya na cewa ƴan bidnga sun kashe aƙalla mutum 49 a wata kasuwa a garin Goronyo na jihar. Wasu ganau sun tabbatar wa da BBC labarin inda suka ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da yamma, yayin da mutanen ke cin babbar kasuwar Goronyon. Mutanen waɗanda suka buƙaci a sakaya sunayensu saboda tsaro sun ce ƴan bindigar sun afka wa kasuwar ne a yayin da ta cika makil da masu hada-hada daga sassan jihar da ma wasu yankunan. "Ƴan fashin sun zo ne da misalin ƙarfe 4.30 zuwa biyar na yamma suka zagaye kasuwar suka buɗe wuta ta kowane ɓangare," in ji ganau ɗin. Majiyarmu ta yi ƙoƙarin jin ta bakin rund8nar ƴan sanda jihar, amma ba mu samu mai magana da yawun ƴan sanda ba a kiran waya da aka yi ta yi masa. Ya ƙara da cewa "Mutane duk suka ruɗe wasu sun kwakkwanta a ƙasa don gudun harbin ya same su, yayin da wasu suka gudu amma masu tsautsayi sun rasa rayukansu." Ganau ɗin sun ce an ƙidaya gawa 49 yayin

PDP za ta 'Kwace mulki daga hannun APC a zaben 2023 - Inji Atiku Abubakar

Alh. Atiku Abubakar Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam'iyyar PDP, Mai adawa, za ta karbi mulki daga hannun jam'iyyar APC, mai mulki, a zaben shekarar 2023. Atku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a dandalin Mahmud Ribadu, Yola, wurin za'ben shugabannin  jam'iyyar PDP na jiha. Ya yi kira ga 'yan siyasa da su mutunta dokokin jam'iyya, na za'be, da Kuma na kundin tsarin mulkin kasar wajen zaben shugabannin jam'iyya, yana mai cewa dimokradiyya na iya 'dorewa ne a cikin yanayi na 'yanci da adalci

Shirin Kare Hakkin Bill"adama Da Tatattalin Arzikin Kasa Ta Maka Buhari A Kotu

Shirin Kare Hakkin Bil Adama Da Tattalin Arzikin Ƙasa Ta Maka Buhari Kotu, Tana Son Shirin Sa Ido Kan Kiran Waya, Sakonnin WhatsApp Da Aka Bayyana Ba Bisa Ka’ida Ba   Shirin Kare Hakkin Bil Adama da Tattalin Arzikin Kasa ya shigar da kara kan Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), inda ya nemi kotu ta “bayyana shirin da doka ta saba da tsarin mulkin da gwamnati ta bi don bin diddigin, katsewa da sa ido kan sakonnin WhatsApp, kiran waya,  da sakonnin tes na 'yan Najeriya da sauran mutane, saboda yana matukar yin barazana da keta hakkin kare sirrin. " Karar ta biyo bayan shawarar da ke cikin Dokar Kasafin Kudin da aka sanya hannu a watan Yuli 2021 don kashe N4.87bn don sa ido kan kira da sakonni.  Adadin kudin na daga cikin karin kasafin kudin N895.8bn da majalisar dokokin kasar ta amince da shi. A cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1240/2021 da aka shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, SERAP na neman “umurnin har ab

Gwamnan Jihar Neja zai hada Hannu da masu saka jari domin cigaban jihar

Gwamna Sani Bello Na JIHAR Niger  Zai Haɗa Hannu Da Masu Saka Hannu Jari Domin Samun Cigaban A Jihar Daga: Abdul Ɗan Arewa A wani bangare na shirinta na saka hannun jari na Kasashen waje kai tsaye (FDI), gwamnatin Gwamna Abubakar Sani Bello tana jan hankalin masu saka hannun jari da ke son yin hadin gwiwa da jihar a fannoni da yawa da za su haifar da ci gaba da ci gaban jihar. Gwamna Sani Bello, a taron UNLOCK AFRICA na gefe na masu saka hannun jari da aka gudanar a Cibiyar Daraktoci, 116 Pall Mall London, sun yi tattaunawa mai ma'ana tare da abokan huldar ci gaba da dama da masu saka hannun jari a fannonin aikin gona, ilimi, ababen more rayuwa, tallafin makamashi, hakar ma'adinai da yawon shakatawa da sauransu.  . Gwamnan ya yarda cewa haɗin gwiwa yana da mahimmanci don sanya Afirka da jihar Niger musamman yanayin kasuwanci mai buɗewa ga masu saka hannun jari na Burtaniya don shigowa yana mai jaddada cewa jihar ita ce zaɓi mafi dacewa don kasuwancin dun

An Cafke Malamar Makarantar Da Ta Yiwa Yaro Ɗan Shekara 15 Fyaɗe

Wannan itace matar da hukumar 'yan sanda ke tuhuma da yiwa wani yaro Fyade. Bambarakwai, wai namiji da sunan Hajara,  Duk da Tuhumar da jami'ai ke yiwa matar, a bangare guda *yaron ya bayyana cewa ba fyaɗe ta mishi ba, da son rainsa suka yi lalata. An kama matar ne dauke da ciki niki-niki bayan da tawa wani ƙaramin yaro dan shekaru 15 fyaɗe. Matar mai suna Heiry Calvi dake karantarwa a makaranta dake Florida ta ƙasar Amurka na fuskantar tuhumar cin zarafin ƙaramin yaro. Sai dai yaron yace ba fyaɗe ta masa ba, da son ransa suka yi lalatar, amma an sanar da shi cewa doka bata yarda da hakan ba, har sai ya kai shekaru 18. An dai kasa tantance cikin na wanene, amma dai ƴan sanda sun kama matar suna bincike. Mu dai anan sadai muce... Can ga su Gada, Wai Zomo yaji kidan 'yan farauta.

Tabbas zan iya komawa APC, Kwankwaso

Tabbas Zan Koma Jam,iyar APC Idan Har Akamin Alkawarin Kujerar Mataimakin Shugaban Kasa Azaben 2023, Cewar Kwankwaso.  Wato jama,a yanzu haka majiyar mu ta labarta mana cewa tsohon gwamnan jihar kano sanata rabi,u musa kwankwaso yama jam,iyar APC albishir da cewa idan har jam,iyar tamai alkawarin mataimakin shugaban kasa 2023 tare da masa alkawarin barin tafiyar kwankwasiya a cikin Nijeriya babu shekka zai koma jam,iyar ta APC. Kamar yadda muka samu labarin cewa sabbin rahotanni sun fito game da shirin tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso na komawa APC Wasu majiyoyi masu ƙarfi sun bayyana cewa Kwankwaso ya kafa wa wakilan APC wasu sharuɗɗa kafin ya koma jam'iyyar ta APC Kamar yadda wata majiya ta sheda mana cewa tun bayan kammala wa'adin mulkin Kwankwaso da Ganduje a 2015, har yanzu Ganduje da Kwankwaso wanda suka kasance abokan juna basa shiri amma ana kyautata zatan zasu shirya gabanin babban zaben 2023 Rahotanni sun bayyana wasu dalilai da yasa har zuwa yanzun tsohon g

EFCC ta ƙaddamar da sabon salon yaƙi da rashawa a Najeriya

Shugaban EFCC Abdurrashid  Bawa Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya ce hukumar za ta fifita daƙile aikata laifuka kafin a aikata su Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta ce ta ɓullo da wani sabon salon daƙile ayyukan rashawa, inda za ta fi mayar da hankali kan rigakafin daƙile laifin kafin a aikata shi. A cewar Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa, daga yanzu hukumar za ta fi mayar da hankali wajen haɗa kai da abokan hulɗarta musamman na ƙasashen waje domin yaƙi da ayyukan rashawa. Da yake magana yayin taron ƙaddamar da sabon tsarin aikin a Abuja, Abdulrasheed Bawa ya ce sabon tsarin na 2021 zuwa 2025 an ciro shi ne daga kundin muradai na EFCC na shekarar 2013 zuwa 2018. "Sabon salon ya fi fifita rigakafi (hana faruwar laifi) a matsayin hanya mafi sauƙin daƙile rashawa fiye da yin hukunci," a cewarsa kamar yadda mujallar EFCC ta mako-mako ta ruwaito. Ya ƙara da cewa sabon tsarin zai fifita tattara bayanan sirri da gurfanar da masu laifi a gaban kotu

Jam'iyyar APC zata wargaje a Kano. Inji Shekarau

    Sen. Mal. Ibrahim Shekarau Sakamakon rikicin da ya barke a jam'iyyar APC, Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta kira taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar Gwamna Ganduje ya karanto sunayen mutanen da Gwamnatin Kano ta basu mukamai na jam'iyya a matakin jiha wanda zata tabbatar dasu gobe Asabar idan Allah Ya kaimh A wajen taron da ya gabata jiya, Gwamna Ganduje ya keta alfarmar tsohon Gwamnan jihar Kano, kuma Sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano) inda ya kirashi da: -Makaryaci -Mai karbe-karbe -Banza Bakwai Hakika Gwamna Ganduje ya tafka babban kuskure da ya karbi shawaran miyagun da suke jikinsa har yake ganin zai iya ja da Malam Ibrahim Shekarau ya kai labari A jihar Kano, bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso babu wanda ya kai Malam Ibrahim Shekarau yawan masoya mabiya, nima Datti Assalafiy a dalilin Malam Ibrahim Shekarau na shigo yabon Gwamna Ganduje Kuma na tabbata imba don Malam Ibrahim Shekarau ya

Sanata Uba Sani ya Gina Makarantun ilimin fasahar Sadarwar zamani a mazabar sa

  A jihar kaduna A kokarin sa na Samar da ingantaccen ilimin zamani ga matasan ‘yan mazabarsa Sanata Uba Sani ya gina tare da samar da kayan aikin cibiyoyin Fasahar Sadarwar Zamani ICT a wasu kananan hukumomi cikin bakwai da Sanatan ke wakiltar a majalisar dattijan Nageriya An Samar da cibiyoyin ne a Makarantun da Suka ha’da da… 1. Maimuna Guarzo sakandirin gwamnatin dake Tudun Wada, a Kaduna ta Kudu, 2. Makarantar sakandaren gwamnati, Kawo, Kaduna ta Arewa da kuma 3. Makarantar sakandaren gwamnati, Turonku, karamar hukumar Igabi. (Ana Kan aiki) Samar da wannan makaratun zai ba wa malamai da ɗaliban Samun damar zama masu ilimin kwamfuta domin shiga jerin sahun sauran mutanen zamanin masu ilimin fasahar Zamani a duk matakan duniya. A Cikin ko wacce Makaranta an Samar da na’urori masu kwakwalwa (Computer) har guda ‘dari biyar 500, Jimulla dubu da ‘dari biyar 1,500. Ana sa ran Sanatan zai Samar da irin wannan makaratun a duk fa’din kananan hukumomin da yake wakilta a jihar kaduna. Anfanin

'Yan bindiga na karbar dafaffen abinci a matsayin kudin fansa a Jihar Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta dauki wasu tsauraran matakai domin yaki da 'yan bindiga.  Yanzu haka ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna sun bukaci a rika ba su dafaffen abinci a matsayin kudin fansa kafin sakin mutanen da suka yi garkuwa da su. Rahotanni na cewa, ‘yan bindigar sun janye daga kaddamar da hare-hare kan garuruwan jihar tun bayan da gwamnatin ta haramta cin kasuwannin mako-mako a wani bangare na daukar matakin magance matsalar tsaro. Daya daga cikin shugabannin matasan kauyukan Birnin Gwari Babangida Yaro ya shaida wa Jaridar Daily Trsut cewa, tun lokacin da gwamnati ta haramta cin kasuwannin, ‘yan bindigar ke neman a rika ba su dafaffen abinci a duk lokacin da suka sace mutun. Yaro ya kara da cewa, matakin hana sayar da man fetur a yankin, shi ma ya taimaka wajen takaita zirga-zairga. A cewarsa, an samu kwarya-kwaryar zaman lafiya a kauyukan Damari da Kuyello da Kutemashi saboda ‘yan bindigar sun daina kaddamar da farmaki, yayin da suka tare a

Jerin sunayen 'yan Nigeria 11 da aka kama a Amurka kan almundahanar kudi da damfarar mutane fiye da 50

An kama wasu 'yan Nigeria 11 a Amurka bisa laifuka na almundahar kudade Laifukan da suka aikata sun hada da damfarar kamfanoni da mutane ta hanyar soyayya Masu bincike sun ce za a gurfanar da su a kotu domin su girbi abin da suka shuka, Hukumar binciken shari'a na Amurka ya gurfanar da wasu 'yan Nigeria 11 a kotu kan zarginsu da hada baki wurin aikata almundahar kudade, damfara ta banki da satar kudade da sunan wasu. A ranar Laraba ne Attoni na Kudancin New York, Damian Williams da Jam'in FBI mai kula da New York, Patrick J, Freancy suka sanar da sunayen 'yan Nigeria 11 da ke da hannu wurin karkatar da miliyoyin daloli daga damfarar imel da damfarar soyayya.  EFCC Ta Gurfanar Da Yarima Gaban Kotu EFCC ta gurfanar da Yarima a gaban kotu kan badakalar N35.5m 'Yan Nigeria 11 da aka gurfanar a Amurka kan almundahar kudi da damfarar mutane fiye da 50. Hukumar binciken shari'a na Amurka ta bayyana hakan a ranar Laraba kamar yadda ya zo a ru

Dokar hana shiga ofis kan korona a Najeriya na tayar da hanakaliMintuna 9 da suka wuceAna yi wa wani allurar rigakafin korona

Dokar hana shiga ofis kan korona a Najeriya na tayar da hanakali Mintuna 9 da suka wuce Ana yi wa wani allurar rigakafin korona Bayan da gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa daga ranar daya ga watan Disamba duk wani ma'aikacin gwamnatin ba za a bar shi ya shiga ofis ba sai ya nuna shedarsa ta yin rigakafin korona ko kuma shedar ba ya dauke da cutar, ma'aikata da dama na bayyana ra'ayoyin daban-daban. Sakataren Gwamnatin wanda kuma shi ne shugaban kwamitin da shugaban kasar ya kafa kan yaki da korona Boss Mustapha ne ya sanar da matakin a yayin zaman ƴan kwamitin a Abuja ranar Laraba 13 ga watan Oktoba 2021. Jaridar Daily Trust ta ambato wani bangare na sanarwar na cewa " daga ranar 1 ga watan Disambar 2021, gwamnatin tarayya za ta bukaci ma'aikatanta su nuna shaidar cewa an yi musu allurar rigakafi ko kuma sakamakon da ke nuna cewa ba su dauke da cutar wanda bai wuce sa'a 72 ba kafin su shiga ofis." A cewar Sakataren Gwamnatin, kididdig