Skip to main content

Allah ya yi wa jikar Ahmadu Bello Sardauna ta farko rasuwa


Allah ya yi wa Hajiya Hadiza Shehu Kangiwa, jikar Sardauna ta farko rasuwa
Marigayiyan ta rasu ne tana da shekaru 61 a duniya kuma ta bar 'ya'ya guda uku
An yi mata sallar jana'iza a gidan Sardauna da ke Diori Hammani road a Sokoto

Jikar tsohon Firimiyan tsohuwar Yankin Arewacin Nigeria, Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto ta riga mu gidan gaskiya.

Hajiya Hadiza ta rasu ne a Sokoto bayan fama da fajeruwar rashin lafiya kamar yadda ya Illela Daily Post ta samu labari.

Marigayiyar diyar Wamban Kano ne, Abubakar Dan Maje.

Hajiya Hadiza ta auri tsohon gwamnan tsohuwar jihar Sokoto, Shehu Kangiwa.
An haife ta ne a shekarar 1960, shekarar da Najeriya ta samu 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

Ta rasu ta bar 'ya'ya uku kuma an yi mata sallar jana'iza a gidan marigayi firimiyan arewa da ke Diori Hammani road a Sokoto.

Yar Tafawa Balewa ta tabbatar da rasuwar Hajiya Hadiza
Jaridar Neptune Prime ta ruwaito cewar kawarta, Hajiya Binta Tafawa Balewa, yar firimiyan farko kuma tilo na Nigeria, Alhaji Abubakar Tafawa Balewa:

"Hajiya Hadiza Shehu Kangiwa matar marigayi Alhaji Shehu Kangiwa, tsohon gwamnan jihar Sokoto ne.

"Ita ce jikar Sardauna ta farko kuma 'yar babban 'yarsa, Hajiya Inno Ahmadu Bello.
"Mahaifin ta shine Wamban Kano, marigayi Abubakar Dan Maje, babban dan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na I."
Wani daga cikin 'yan uwanta, Alhaji Shehu Aliyu Maradun ya ce marigayiyar ta kasance mai saukin kai duk da irin girma da daraja na gidan da ta fito.

Comments

Popular posts from this blog

An Cafke Malamar Makarantar Da Ta Yiwa Yaro Ɗan Shekara 15 Fyaɗe

Wannan itace matar da hukumar 'yan sanda ke tuhuma da yiwa wani yaro Fyade. Bambarakwai, wai namiji da sunan Hajara,  Duk da Tuhumar da jami'ai ke yiwa matar, a bangare guda *yaron ya bayyana cewa ba fyaɗe ta mishi ba, da son rainsa suka yi lalata. An kama matar ne dauke da ciki niki-niki bayan da tawa wani ƙaramin yaro dan shekaru 15 fyaɗe. Matar mai suna Heiry Calvi dake karantarwa a makaranta dake Florida ta ƙasar Amurka na fuskantar tuhumar cin zarafin ƙaramin yaro. Sai dai yaron yace ba fyaɗe ta masa ba, da son ransa suka yi lalatar, amma an sanar da shi cewa doka bata yarda da hakan ba, har sai ya kai shekaru 18. An dai kasa tantance cikin na wanene, amma dai ƴan sanda sun kama matar suna bincike. Mu dai anan sadai muce... Can ga su Gada, Wai Zomo yaji kidan 'yan farauta.

Ganduje ya bai wa makaho aiki saboda bajintarsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bai wa Ɗahuru Abdulhamid Idris wanda makaho ne, aikin koyarwa a gwamnatin jihar. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Sakataren Labarai na gwamnatin jihar, Abba Anwar ya fitar a ranar Lahadi. Kafin wannan lokaci, Ɗahuru ya kasance yana aikin koyarwa na sa-kai ba tare da ana biyansa wani albashi ba. Sanarwar ta ce bayan da Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Muhammadu Sanusi Kiru, ya jagoranci Ɗahuru zuwa gaban Ganduje ne, a nan Ganduje ya bada umarnin a ɗauke shi aiki sannan a tura shi Makarantar Nakasassu da ke Tudun Maliki don ya ci gaba koyarwa. Yayin ganawar tasu, Ganduje ya yaba wa ƙoƙarin Ɗahuru musamman ma ganin yadda bai bari lalurar makanta ta hana shi bada tasa gudunmawa ga cigaban fannin ilimin jihar ba. Bisa wannan dalili ne Gwamna Ganduje ya ce, “Lallai ka taki matakin da ya dace a rayuwarka. Gwamnatin jihar Kano ta ba ka aikin koyarwa. Kuma na umarci Kwamishinan Ilimi da a tura ka zu...

Kamfanin Facebook Zai Canza Sunan Sa.

LABARU DA DUMI-DUMIN SU! Shahararren dandalin sada zumunta na Facebook Inc yana shirin sake sunan kansa da sabon suna a mako mai zuwa, shafin yanar gizo na fasahar Amurka Verge ya ruwaito a ranar Talata, inda ya ambaci wata majiya da ke da masaniya kai tsaye kan lamarin.  Babban Jami'i kuma Shugaban Facebook Mark Zuckerberg yana shirin yin magana game da canjin sunan a taron haɗin gwiwa na kamfani na shekara -shekara a ranar 28 ga Oktoba, amma ana iya bayyana shi da wuri, inji rahoton Verge. Labarin na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin ke fuskantar karuwar sanya ido daga gwamnati a Amurka kan harkokin kasuwancinsa.  Sake canza sunan zai sanya aikace -aikacen kafofin watsa labarun Facebook a matsayin ɗayan samfura da yawa a ƙarƙashin kamfanin, wanda kuma zai kula da sauran manhajojin sa kamar Instagram, WhatsApp, Oculus da sauran su, in ji rahoton Verge.  Ba sabon abu bane a Silicon Valley don kamfanoni sun canza sunayensu yayin da suke neman fadada ayyukan ...