Skip to main content

Musulmai Sun Yi Martani Ga Gumi Bayan Sukar Da Yayi Akan Maulud



Musulman Najeriya sun mamaye shafin Facebook na Dr. Ahmad Gumi.

shahararren mai fafutukar kare hakkin ‘yan fashin daji bayan yayi suka ga maulidi a shafin a daidai lokacin da musulman suke  tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad SAWA. 

A kowace shekara a cikin watan Rabi’ul Awwal, Musulmin duniya suna tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad ta hanyar karanta Alƙur’ani mai girma, ƙasidun yabo ya Annabi da karanta tarihin rayuwar sa.

Shafin Dr. Gumi na Facebook ya samu sharhi sama da 600 har zuwa lokacin nan a tare da cewa suka yayi akan maulidin, amma da yawan su suna rubuta "Happy Maulud,"  duk da sun karanta sukar da yayi.  

Karantarwar Dr Gumi tana fuskantar tsaiko da rashin tasiri akan mutane bayan ya karkatar da hankalin sa daga taimakon waɗanda rikicin yan fashin daji ya rutsa da su a arewa maso yammacin Najeriya zuwa neman haƙƙin masu aikata laifin.

Comments

Popular posts from this blog

An Cafke Malamar Makarantar Da Ta Yiwa Yaro Ɗan Shekara 15 Fyaɗe

Wannan itace matar da hukumar 'yan sanda ke tuhuma da yiwa wani yaro Fyade. Bambarakwai, wai namiji da sunan Hajara,  Duk da Tuhumar da jami'ai ke yiwa matar, a bangare guda *yaron ya bayyana cewa ba fyaɗe ta mishi ba, da son rainsa suka yi lalata. An kama matar ne dauke da ciki niki-niki bayan da tawa wani ƙaramin yaro dan shekaru 15 fyaɗe. Matar mai suna Heiry Calvi dake karantarwa a makaranta dake Florida ta ƙasar Amurka na fuskantar tuhumar cin zarafin ƙaramin yaro. Sai dai yaron yace ba fyaɗe ta masa ba, da son ransa suka yi lalatar, amma an sanar da shi cewa doka bata yarda da hakan ba, har sai ya kai shekaru 18. An dai kasa tantance cikin na wanene, amma dai ƴan sanda sun kama matar suna bincike. Mu dai anan sadai muce... Can ga su Gada, Wai Zomo yaji kidan 'yan farauta.

Ganduje ya bai wa makaho aiki saboda bajintarsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bai wa Ɗahuru Abdulhamid Idris wanda makaho ne, aikin koyarwa a gwamnatin jihar. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Sakataren Labarai na gwamnatin jihar, Abba Anwar ya fitar a ranar Lahadi. Kafin wannan lokaci, Ɗahuru ya kasance yana aikin koyarwa na sa-kai ba tare da ana biyansa wani albashi ba. Sanarwar ta ce bayan da Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Muhammadu Sanusi Kiru, ya jagoranci Ɗahuru zuwa gaban Ganduje ne, a nan Ganduje ya bada umarnin a ɗauke shi aiki sannan a tura shi Makarantar Nakasassu da ke Tudun Maliki don ya ci gaba koyarwa. Yayin ganawar tasu, Ganduje ya yaba wa ƙoƙarin Ɗahuru musamman ma ganin yadda bai bari lalurar makanta ta hana shi bada tasa gudunmawa ga cigaban fannin ilimin jihar ba. Bisa wannan dalili ne Gwamna Ganduje ya ce, “Lallai ka taki matakin da ya dace a rayuwarka. Gwamnatin jihar Kano ta ba ka aikin koyarwa. Kuma na umarci Kwamishinan Ilimi da a tura ka zu...

Kamfanin Facebook Zai Canza Sunan Sa.

LABARU DA DUMI-DUMIN SU! Shahararren dandalin sada zumunta na Facebook Inc yana shirin sake sunan kansa da sabon suna a mako mai zuwa, shafin yanar gizo na fasahar Amurka Verge ya ruwaito a ranar Talata, inda ya ambaci wata majiya da ke da masaniya kai tsaye kan lamarin.  Babban Jami'i kuma Shugaban Facebook Mark Zuckerberg yana shirin yin magana game da canjin sunan a taron haɗin gwiwa na kamfani na shekara -shekara a ranar 28 ga Oktoba, amma ana iya bayyana shi da wuri, inji rahoton Verge. Labarin na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin ke fuskantar karuwar sanya ido daga gwamnati a Amurka kan harkokin kasuwancinsa.  Sake canza sunan zai sanya aikace -aikacen kafofin watsa labarun Facebook a matsayin ɗayan samfura da yawa a ƙarƙashin kamfanin, wanda kuma zai kula da sauran manhajojin sa kamar Instagram, WhatsApp, Oculus da sauran su, in ji rahoton Verge.  Ba sabon abu bane a Silicon Valley don kamfanoni sun canza sunayensu yayin da suke neman fadada ayyukan ...