Skip to main content

Dokar hana shiga ofis kan korona a Najeriya na tayar da hanakaliMintuna 9 da suka wuceAna yi wa wani allurar rigakafin korona

Dokar hana shiga ofis kan korona a Najeriya na tayar da hanakali
Mintuna 9 da suka wuce
Ana yi wa wani allurar rigakafin korona
Bayan da gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa daga ranar daya ga watan Disamba duk wani ma'aikacin gwamnatin ba za a bar shi ya shiga ofis ba sai ya nuna shedarsa ta yin rigakafin korona ko kuma shedar ba ya dauke da cutar, ma'aikata da dama na bayyana ra'ayoyin daban-daban.
Sakataren Gwamnatin wanda kuma shi ne shugaban kwamitin da shugaban kasar ya kafa kan yaki da korona Boss Mustapha ne ya sanar da matakin a yayin zaman ƴan kwamitin a Abuja ranar Laraba 13 ga watan Oktoba 2021.

Jaridar Daily Trust ta ambato wani bangare na sanarwar na cewa " daga ranar 1 ga watan Disambar 2021, gwamnatin tarayya za ta bukaci ma'aikatanta su nuna shaidar cewa an yi musu allurar rigakafi ko kuma sakamakon da ke nuna cewa ba su dauke da cutar wanda bai wuce sa'a 72 ba kafin su shiga ofis."

A cewar Sakataren Gwamnatin, kididdigar gwaji ta sama da makonni hudu da suka wuce ta nuna cewa yayin da bazuwar cutar ke raguwa a wasu jihohi, tana karuwa ne a wasu jihohin.

ra'ayoyin wasu daga cikin ma'aikata sa dai mun sakaya sunayensu;
Daga jihar Jigawa wannan cewa ya yi, ''matakin ya yi tsauri, mutane abin da suke fama da shi yanzu shi ne albashi kansa ba ya isar ma'aikata.
"Kuma tuni ai daman matakin da gwamnti ta dauka cewa ma'aikacin da yake daga mataki na 12 zuwa kasa kada ya je aiki, idan dai harkar korona ake magana ai ya isa ya yi magani tun da korona ba ta son cudayya to wannan matakin kadai ya isa, to kuma har a ce sai ka je ka yi wannan allura idan babu ita ba za ka je ofis ba wannan matakin ya yi tsauri gaskiyar magana.

"Kuma zai iya kara sawa mutane hankalinsu ya sake barin gwamnatin gaba daya."
Ana rigakafi
Daga Abuja: "Tun da dai matsala ce wadda ta shafi duniya baki daya ta wannan annoba ta korona ko da yake ita gwamnatin tana so ta yi amfani da wadanda take da iko a kansu, kasancewar wasu jihohi sun yi kokarin su sa a yi amma aka samu tirjiya wannan mataki zai sa a samu mutane da yawa da za su yi rigakafin.

To amma gaskiya gwamnati kamata ya yi ta wayarwa da mutane kai sosai a kan allurar domin har yanzu mutane da dama har ma da ƴan Boko kar ka yi mamaki wadanda suke nuna shakku ko ma zargin cewa rigakafin yana da lahani zai jawo kaza zai jawo kaza. Ko da yake ni na riga na yi nawa.''

Wata ma'aikaciya daga Abuja cewa ta yi, '' Ina ganin ba abu ne da ya zama dole ba, domin hukumar lafiya ta duniya ta riga ta ce allurar rigakafin ba dole ba ce.

"Idan dai har suna son su sa mutane su yi rigakafin ne to bai kamata su tilasta wa mutane su ce lalle sai an yi ba. Mutane da yawa kowa yana da dalilin da ya sa bai yi ba.
"Idan gwamnti ta ce lalle kowa sai ya yi to ta shiga hakkin mutane. Ni dai a yanzu ban yi b kuma ban san abin da zan yi ba idan lokacin d gwamnatin ta yi ya zo.

"Ina fatan lamarin da ba zai kai a ce gwamnati ta tilasta yin allurar ba. Ina fatan za ta sauya shawara kafin lokacin. Kuma ma allurar har guda nawa ake da ita a Najeriya, da za a tilasata wa jama'a?
"Ai allurar ma babu ita wadatacciya a kasar. Gwamnatin ba ta ma shirya wa bin da take magana a kai ba."
WHO: 'Kasashen Afirka na baya a riga-kafin korona'
Abin da ya sa allurar riga-kafin korona miliyan 241 za su yi kwantai
Korona: Italiya ta yi dokar tilasta ma'aikata nuna shedar rigakafi
Wannan kuwa cewa take; "Eh to yana da kyau in dai har zai zama matakin kawo karshen yaduwar cutar koronar ina ganin ya dace tun da har yanzu gwamnati ba ta bayar da umarnin ma'aikata ƴa matakin 12 zuwa kasa su koma aiki ba.

"Ina ga duk yana daga cikin abin da ya sa ba su bari kowa da kowa ya koma aiki ba.
Amma idan har matakin zai zama silar da za ta sa kowa ya koma bakin aiki kuma ya samu kariya daga cutar hakan yana da kyau. Tun da gwamnati ta ce akwai allurar kuma har yanzu ana kan kawowa abu ne da kowa ya kamata ya yi.

"Tun da dai an ga cewa ba wai yana da wata illa ba. Yawancin wadanda suka yi ba wata matsala ce ta samesu da za a ce rigakafin ne ya sa mu in ban da yan kananan matsaloli wadanda ko da ma ba rigakafin ba mutum yana iya samunsu," in ji ta.
Wannan layi ne
Martanin shugaban kungiyar likitoci ta Najeriya
Shugaban kungiyar likitoci ta Najeriyar Dr Uja ya yaba da matakin yana cewa umarnin na gwamnati mataki ne da ya dace wajen yaki da cutar ta korona, inda ya kara da cewa abu da ya shafi bukatar kasa da kuma kulawa.

Ya ce akwai bukatar ƴan Najeriya su kare kansu, yana mai karin bayani da cewa umarnin da shugaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa kan yaki da cutar wato Boss Mustapha, kyakkyawan mataki ne na yaki da cutar, wanda kuma ya yi hakan ne ba domin wata muguwar manufa ba, alheri yake nufi da kasar, kamar yadda shugaban kungiyar likitocin ya ce.

Ya ce hakan ya nuna cewa lalle cutar gaskiya ne akwai ta kuma tana nan a tsakanin ƴan Najeriya sosai.
Takunkumi

Zuwa yanzu Najeriya ta samu alkaluman mutane 208,404 da suka kamu da cutar ta korona, da kuma wadanda suka mutu 2,761.
Kasar ta kuma yi wa mutane miliyan biyar daga cikin miliyan 200 rigakafin cutar da magungunan Moderna (MRNA.O) da AstraZeneca (AZN.L) daga wadanda ta samu daga shirin samar da rigakafin na kasashe masu tasowa, COVAX
Haka kuma kasar ta samu allurar rigakafin Johnson & Johnson (JNJ.N) miliyan 1.12 da ta saya daga shirin kungiyar kasashen Afirka kuma tana shirin karbar miliyan 7.7 na Sinopharm (1099.HK) ta hanyar COVAX.

Comments

Popular posts from this blog

An Cafke Malamar Makarantar Da Ta Yiwa Yaro Ɗan Shekara 15 Fyaɗe

Wannan itace matar da hukumar 'yan sanda ke tuhuma da yiwa wani yaro Fyade. Bambarakwai, wai namiji da sunan Hajara,  Duk da Tuhumar da jami'ai ke yiwa matar, a bangare guda *yaron ya bayyana cewa ba fyaɗe ta mishi ba, da son rainsa suka yi lalata. An kama matar ne dauke da ciki niki-niki bayan da tawa wani ƙaramin yaro dan shekaru 15 fyaɗe. Matar mai suna Heiry Calvi dake karantarwa a makaranta dake Florida ta ƙasar Amurka na fuskantar tuhumar cin zarafin ƙaramin yaro. Sai dai yaron yace ba fyaɗe ta masa ba, da son ransa suka yi lalatar, amma an sanar da shi cewa doka bata yarda da hakan ba, har sai ya kai shekaru 18. An dai kasa tantance cikin na wanene, amma dai ƴan sanda sun kama matar suna bincike. Mu dai anan sadai muce... Can ga su Gada, Wai Zomo yaji kidan 'yan farauta.

Ganduje ya bai wa makaho aiki saboda bajintarsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bai wa Ɗahuru Abdulhamid Idris wanda makaho ne, aikin koyarwa a gwamnatin jihar. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Sakataren Labarai na gwamnatin jihar, Abba Anwar ya fitar a ranar Lahadi. Kafin wannan lokaci, Ɗahuru ya kasance yana aikin koyarwa na sa-kai ba tare da ana biyansa wani albashi ba. Sanarwar ta ce bayan da Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Muhammadu Sanusi Kiru, ya jagoranci Ɗahuru zuwa gaban Ganduje ne, a nan Ganduje ya bada umarnin a ɗauke shi aiki sannan a tura shi Makarantar Nakasassu da ke Tudun Maliki don ya ci gaba koyarwa. Yayin ganawar tasu, Ganduje ya yaba wa ƙoƙarin Ɗahuru musamman ma ganin yadda bai bari lalurar makanta ta hana shi bada tasa gudunmawa ga cigaban fannin ilimin jihar ba. Bisa wannan dalili ne Gwamna Ganduje ya ce, “Lallai ka taki matakin da ya dace a rayuwarka. Gwamnatin jihar Kano ta ba ka aikin koyarwa. Kuma na umarci Kwamishinan Ilimi da a tura ka zu...

Kamfanin Facebook Zai Canza Sunan Sa.

LABARU DA DUMI-DUMIN SU! Shahararren dandalin sada zumunta na Facebook Inc yana shirin sake sunan kansa da sabon suna a mako mai zuwa, shafin yanar gizo na fasahar Amurka Verge ya ruwaito a ranar Talata, inda ya ambaci wata majiya da ke da masaniya kai tsaye kan lamarin.  Babban Jami'i kuma Shugaban Facebook Mark Zuckerberg yana shirin yin magana game da canjin sunan a taron haɗin gwiwa na kamfani na shekara -shekara a ranar 28 ga Oktoba, amma ana iya bayyana shi da wuri, inji rahoton Verge. Labarin na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin ke fuskantar karuwar sanya ido daga gwamnati a Amurka kan harkokin kasuwancinsa.  Sake canza sunan zai sanya aikace -aikacen kafofin watsa labarun Facebook a matsayin ɗayan samfura da yawa a ƙarƙashin kamfanin, wanda kuma zai kula da sauran manhajojin sa kamar Instagram, WhatsApp, Oculus da sauran su, in ji rahoton Verge.  Ba sabon abu bane a Silicon Valley don kamfanoni sun canza sunayensu yayin da suke neman fadada ayyukan ...