Skip to main content

Najeriya ta ce ita mamba ce ta Majalisar Ɗinkin Duniya wadda take da dokoki na kare duk wani mutum da ba shi da fasfo na wata ƙasa,

Najeriya ta ce ita mamba ce ta Majalisar Ɗinkin Duniya wadda take da dokoki na kare duk wani mutum da ba shi da fasfo na wata ƙasa, wanda a kan haka ta ƙi amsa buƙatar shugaban Turkiyya ta korar wasu ƴan ƙasarsa.
Rahoto: Comrade Musa Garba Augie.

Fadar Shugaban Najeriya ta yi bayani kan dalilan da suka sa gwamnatin kasar ta ƙi amincewa da bukatar shugaban Turkiyya Racib Tayyeb Erdogan na ba shi hadin kai wajen daukar mataki kan magoya bayan Fathullah Gullen da ƙadarorinsa da ke Najeriya.

Shugaba Recep Tayyip Erdoğan na Turkiyya ya ce wadanda suka shirya yi masa juyin mulki a 2016 suna nan har yanzu a Najeriya suna gudanar da harkokinsu inda ya nemi hadin kan Najeriya wajen murkushe su.

Erdogan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin ziyararsa ta kwana biyu a Najeriya, inda suka tattauna kan batutuwa da yawa na alaƙa tsakaninsa da Shugaba Buhari.

Sai dai ba wannan ne karo na farko da Turkiyya take neman wannan buƙatar ba, ta sha neman hakan ta wajen jakadanta da ke Najeriya, amma gwamnati na yin biris da buƙatar.

Mataimaki na musamman ga shugaban Najeriya kan harkokin yada labarai, Mallam Garba Shehu ya nuna cewa matsayin shugaban kasar na ƙin amsa bukatar shugaban Turkiyya ta rufe makarantu da asibitoci da sauran harkoki na wadanda kasar ke zargi da yunkurin kifar da gwamnati bai sauya ba kamar a baya.

Ita dai gwamnatin Erdogan tana zargin mabiya kungiyar fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke zaune a Amurka Fethullah Gulen da yunkurin kifar da gwamnatinsa, kuma tana daukar makarantu da asibitocin ƴan Turkiyya da ke Najeriya a matsayin na magoya bayan malamin.

Shi dai Fethullah Gulen wanda tsohon makusancin Erdogan ne, ya musanta wannan zargi na yunƙurin, wanda bai yi nasara ba, wanda kuma ya kai ga hallaka farar hula sama da 250, tare da kama dubban mutane da gwamnatin ta zarga da hannu a ciki.

Yawancin wadanda aka zarga da yunkurin jami'an tsaron fadar shugaban kasar ne.

Tun bayan yunkurin Shugaba Erdogan na harin magoy bayan malamin, inda da yawa daga cikin ƴan kasar da ke aiki da gwamnati da ma sojoji suka rasa ayyukansu bisa zargin goyon baya da kungiyar malamin.

A hirarsa da BBC, Garba Shehu ya ce ko a ziyarar baya wadda shugaban na Turkiyya ya zo Najeriya a ranar 1 ga watan Maris na 2016, Erdogan ya gabatar wa da Buhari wannan bukata ta rufe harkokin ƴan kasar tasa da yake zargi da neman hambarar da gwamnatinsa, bisa alkawarin cewa su za su kawo wasu makarantun da asibitoci su maye gurbin wadannan.

Kakakin na Buhari ya ce har a yanzu da shugaban na Turkiyya ya kara gabatar da wannan bukata, amsar da Shugaba Buharin ya ba shi kamar a wancan lokacin ba ta sauya.

"To ai wannan magana da ma ba sabuwa ba ce, ko wancan karo da ya zo, a hakika ya nemi cewa a rufe su makarantu, asibitoci da sauransu su za su kawo sababbi a kafa.

"Amsa da Shugaba Buhari ya bayar a wancan lokaci shi ne, Najeriya ƙawa ce ga Turkiyya muna da dangantaka kyakkyawa tsakaninmu.

"In ma ban da haka babu wata kasa ta duniya da za mu yarda mu nan Najeriya a yi amfani da kasarmu a kafa sansani don cin zarafi ko don a kawo tashin hankali a wata kasa."

"Saboda haka wannan ziyarar da aka kawo wa Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada wannan matsayi nasa bai canja ba," in ji Garba Shehu.

Dangane da cewa ko za a dauki matakin rufe makarantun da asibitocin sai kakakin ya ce, "A'a cewa mu a matsayinmu na mambobi na Majalisar Dinkin Duniya ai akwai ƙa'idoji iri daban-daban da MDD ta ajiye don kare hakki ƴan kasa wadanda ba su da fasfo a ko ina suke a duniya.

"Wannan Majalisar Dinkin Duniya ke musu gata a dauka cewa kasarsu Majalisar Dinkin Duniya ce."

Mataimakin na musamman ga Shugaba Buhari ya kara da bayanin cewa maganar da shugaban na Turkiyya ya yi a dunkule take, "mu ma tamu a dunkule take saboda haka ina ganin akwai kyakkyawar fahimtar juna."

Akwai dai asibitoci da makarantun furamare da na sakandire har ma da jami'a na ƴan Turkiyya a wasu jihohin Najeriya, wadanda Erdogan ke zargin dukkaninsu suna da alaka da magoy bayan Sheikh Gulen.

Abubuwan da ziyarar ta Erdogan ta cimma a Najeriya
A yayin ziyarar ta kwana biyu ta shugaban na Turkiya wanda ya sauka a Abuja ranar Talata 19 ga watan Oktoba 2021, tare da matarsa, Emine Erdoğan.

Kazalika ya zo da ministan harkokin waje, Mevlüt Çavuşoğlu, da ta Muhalli, Fatma Güldemet Sarı, da na tattalin arziki Mustafa Elitaş, da na makamashi, Berat Albayrak, da na tsaro İsmet Yılmaz da kuma manyan 'yan kasuwar kasar.

Kasashen biyu sun kulla yarjeniyoyi kusan guda takwas a tsakaninsu.

Sun hada da takaita karbar haraji a tsakanin kamfanonin kasashen biyu da harkar ma'adanai da batutuwan tsaro da makamashi na wutar lantarki da gas da tallafa wa matasa da kuma harkokin siyasar duniya.

Comments

Popular posts from this blog

Musulmai Sun Yi Martani Ga Gumi Bayan Sukar Da Yayi Akan Maulud

Musulman Najeriya sun mamaye shafin Facebook na Dr. Ahmad Gumi. shahararren mai fafutukar kare hakkin ‘yan fashin daji bayan yayi suka ga maulidi a shafin a daidai lokacin da musulman suke  tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad SAWA.  A kowace shekara a cikin watan Rabi’ul Awwal, Musulmin duniya suna tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad ta hanyar karanta Alƙur’ani mai girma, ƙasidun yabo ya Annabi da karanta tarihin rayuwar sa. Shafin Dr. Gumi na Facebook ya samu sharhi sama da 600 har zuwa lokacin nan a tare da cewa suka yayi akan maulidin, amma da yawan su suna rubuta "Happy Maulud,"  duk da sun karanta sukar da yayi.   Karantarwar Dr Gumi tana fuskantar tsaiko da rashin tasiri akan mutane bayan ya karkatar da hankalin sa daga taimakon waɗanda rikicin yan fashin daji ya rutsa da su a arewa maso yammacin Najeriya zuwa neman haƙƙin masu aikata laifin.

PDP za ta 'Kwace mulki daga hannun APC a zaben 2023 - Inji Atiku Abubakar

Alh. Atiku Abubakar Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam'iyyar PDP, Mai adawa, za ta karbi mulki daga hannun jam'iyyar APC, mai mulki, a zaben shekarar 2023. Atku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a dandalin Mahmud Ribadu, Yola, wurin za'ben shugabannin  jam'iyyar PDP na jiha. Ya yi kira ga 'yan siyasa da su mutunta dokokin jam'iyya, na za'be, da Kuma na kundin tsarin mulkin kasar wajen zaben shugabannin jam'iyya, yana mai cewa dimokradiyya na iya 'dorewa ne a cikin yanayi na 'yanci da adalci

'Yan bindiga na karbar dafaffen abinci a matsayin kudin fansa a Jihar Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta dauki wasu tsauraran matakai domin yaki da 'yan bindiga.  Yanzu haka ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna sun bukaci a rika ba su dafaffen abinci a matsayin kudin fansa kafin sakin mutanen da suka yi garkuwa da su. Rahotanni na cewa, ‘yan bindigar sun janye daga kaddamar da hare-hare kan garuruwan jihar tun bayan da gwamnatin ta haramta cin kasuwannin mako-mako a wani bangare na daukar matakin magance matsalar tsaro. Daya daga cikin shugabannin matasan kauyukan Birnin Gwari Babangida Yaro ya shaida wa Jaridar Daily Trsut cewa, tun lokacin da gwamnati ta haramta cin kasuwannin, ‘yan bindigar ke neman a rika ba su dafaffen abinci a duk lokacin da suka sace mutun. Yaro ya kara da cewa, matakin hana sayar da man fetur a yankin, shi ma ya taimaka wajen takaita zirga-zairga. A cewarsa, an samu kwarya-kwaryar zaman lafiya a kauyukan Damari da Kuyello da Kutemashi saboda ‘yan bindigar sun daina kaddamar da farmaki, yayin da suka tare a...