Skip to main content

Wasu jigajigai a jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC a jihar Yobe


Mataimakin shugaban PDP da wasu manyan shugabanni sun sauya sheƙa zuwa Jam'iyyar APC a jihar Yobe dake Arewa maso gabashin Nigeria.

Mataimakin shugaban PDP reshen jihar Yobe, tare da wasu manyan jiga-jigai sun koma jam'iyyar APC mai mulki
A cewar waɗanda suka sauya shekan, ba bu wani dalili da zai sa su cigaba da zama cikin PDP, saboda shugaban ƙasa na bukatar goyon baya

Gwamna Mai Mala Buni, na jihar Yobe, ya tabbatar musu da cewa ba za'a nuna musu banbanci ba.

Wasu daga cikin shugabannin jam'iyyar hammaya PDP reshen jihar Yobe, tare da mambobi sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Vanguard ta rahoto cewa daga cikin waɗanda suka koma APC har da, mataimakin shugaban PDP na jiha, Alhaji Usman Amale, da mataimakin sakatare, Malam Ahmadu Biriri.

Jaridar Illela Daily Post ta ruwaito cewa gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, shine ya karbi masu sauya shekan ranar Talata a Damaturu.

Gwamna Mai Mala Buni, wanda shine shugaban kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa, ya nuna jin daɗinsa bisa matakin tsoffin jiga-jigan PDP.

Kun ɗauki matakin da ya dace - Buni
Gwamna Mai Mala Buni ya godewa mutanen bisa ɗaukar matakin shigowa APC domin bada gudummuwarsu wajen gyara Najeriya.

Gwamnan yace:

"A halin yanzu jam'iyyar APC ta maida hankali wajen haɗa kan Najeriya da kuma samar da cigaba ga yan ƙasa."
"A koda yaushe muna maraba da manyan masu ruwa da tsaki a Najeriya daga kowane sashi, al'ada da kuma addinai."
"Hanyar warware matsalolin Najeriya ya dogara ne a kan siyasa, saboda haka ya zama wajibi mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen haɗa kawunan mu, domin cigaban ƙasar mu."


Comments

Popular posts from this blog

EFCC ta ƙaddamar da sabon salon yaƙi da rashawa a Najeriya

Shugaban EFCC Abdurrashid  Bawa Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya ce hukumar za ta fifita daƙile aikata laifuka kafin a aikata su Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta ce ta ɓullo da wani sabon salon daƙile ayyukan rashawa, inda za ta fi mayar da hankali kan rigakafin daƙile laifin kafin a aikata shi. A cewar Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa, daga yanzu hukumar za ta fi mayar da hankali wajen haɗa kai da abokan hulɗarta musamman na ƙasashen waje domin yaƙi da ayyukan rashawa. Da yake magana yayin taron ƙaddamar da sabon tsarin aikin a Abuja, Abdulrasheed Bawa ya ce sabon tsarin na 2021 zuwa 2025 an ciro shi ne daga kundin muradai na EFCC na shekarar 2013 zuwa 2018. "Sabon salon ya fi fifita rigakafi (hana faruwar laifi) a matsayin hanya mafi sauƙin daƙile rashawa fiye da yin hukunci," a cewarsa kamar yadda mujallar EFCC ta mako-mako ta ruwaito. Ya ƙara da cewa sabon tsarin zai fifita tattara bayanan sirri da gurfanar da masu laifi a gaban kotu...

Ganduje ya bai wa makaho aiki saboda bajintarsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bai wa Ɗahuru Abdulhamid Idris wanda makaho ne, aikin koyarwa a gwamnatin jihar. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Sakataren Labarai na gwamnatin jihar, Abba Anwar ya fitar a ranar Lahadi. Kafin wannan lokaci, Ɗahuru ya kasance yana aikin koyarwa na sa-kai ba tare da ana biyansa wani albashi ba. Sanarwar ta ce bayan da Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Muhammadu Sanusi Kiru, ya jagoranci Ɗahuru zuwa gaban Ganduje ne, a nan Ganduje ya bada umarnin a ɗauke shi aiki sannan a tura shi Makarantar Nakasassu da ke Tudun Maliki don ya ci gaba koyarwa. Yayin ganawar tasu, Ganduje ya yaba wa ƙoƙarin Ɗahuru musamman ma ganin yadda bai bari lalurar makanta ta hana shi bada tasa gudunmawa ga cigaban fannin ilimin jihar ba. Bisa wannan dalili ne Gwamna Ganduje ya ce, “Lallai ka taki matakin da ya dace a rayuwarka. Gwamnatin jihar Kano ta ba ka aikin koyarwa. Kuma na umarci Kwamishinan Ilimi da a tura ka zu...

PDP za ta 'Kwace mulki daga hannun APC a zaben 2023 - Inji Atiku Abubakar

Alh. Atiku Abubakar Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam'iyyar PDP, Mai adawa, za ta karbi mulki daga hannun jam'iyyar APC, mai mulki, a zaben shekarar 2023. Atku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a dandalin Mahmud Ribadu, Yola, wurin za'ben shugabannin  jam'iyyar PDP na jiha. Ya yi kira ga 'yan siyasa da su mutunta dokokin jam'iyya, na za'be, da Kuma na kundin tsarin mulkin kasar wajen zaben shugabannin jam'iyya, yana mai cewa dimokradiyya na iya 'dorewa ne a cikin yanayi na 'yanci da adalci