Skip to main content

Buhari ya fusata da kisar gillar da aka yi wa masu cin kasuwa a garin Goronyo dake gabashin jihar Sokoto.


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi matukar fusata da kisan gillar da aka yi wa masu cin Kasuwa a Goronyo, Jihar Sokoto inda ya aika wa ƴan bindiga sakon ‘Ta su ta kare’ ranar Litinin.

Kakakin fadar shugaban ƙasa, Garba Shehu a wata takarda daga fadar shugaba Buhari ranar Litinin ya bayyana cewa shugaban Buhari ya fusata matuka da kisan da aka yi wa ƴan kasuwa da basu ji ba basu gani ba a kasuwar goronyo.

Buhari ya ce wannan karon ƴan bindigan sun kai gwamnati maƙura kuma sun siya da kuɗin su domin sai sun gwammace kiɗa da karatu nan ba da daɗewa ba.

” Ko a yanzu ba su ji da daɗi daga dakarun Najeriya ta sama da kasa ba. Hakan yasa suke bin mutanen da basu ji ba basu gani suna kashe su. Wannan abu ya kai mu makura yanzu kuma lallai su kwana da shirin ta su ta kare.

Harin Goronyo

A kasuwar Goronyo jihar Sokoto dake ci mako-mako ne ‘yan bindiga suka buda wa mutane wuta inda suka kashe mutum sama da 30 sannan da dama sun ji rauni.

Wannan hari ya auku ne kwanaki 12 da wasu ‘yan bindiga suka kashe mutane a kasuwar Unguwar Lalle dake karamar hukumar Sabon Birni.

A jihar Sokoto kananan hukumomin Goronyo, Isa, Sabon Birni da Raba wurare ne da ‘yan bindiga suka addaba da hare-hare.

Wani dake kare rajin dan Adam a jihar Sokoto Basharu Guyawa ya ce maharan d suka kau su akalla 200 sai da suka zagaye kasuwar sannan suka bude wa mutane wuta ta ko ina.

Ya ce ‘yan bindigan sun dauki awowi suna barin wuta a kasuwar, ba a dai iya fayyace ko mutum naya suka sheka lahira a dalilin wannan hari ba, saidai an kiyasta cewa an ga gawarwaki sama da 30 wanda aka kashe nan take.

Wani mazaunin garin kuma tsohon ma’aikacin gwamnati Bashir Adamu ya ce ba za su taba manta wa da wannan rana ta Lahadi ba.

Ya ce maharan sun kashe mutum sama da 30 sannan mutum 20 sun ji rauni.

A ziyarar jaje da babban ahfsan sojojin Najeriya Faruk Yahaya ya kai wa gwamnan Sokoto ranar Litinin, ya tabbatar wa gwamna AMinu Tambuwal cewa za a ci gaba da suburbudar yan bindigan a lo’ina suka a fadin kasar nan.

” Wannan wannan mummunar hari ne da ba shi misaltuwa da komai. Ina kira ga rundunar soji da ta turo karin jami’ai jihar domin gamawa da ‘yan bindigan da suka addabi mutanen yankin jihar.

Rahoto: Salisu Idris Waziri

Comments

Popular posts from this blog

Musulmai Sun Yi Martani Ga Gumi Bayan Sukar Da Yayi Akan Maulud

Musulman Najeriya sun mamaye shafin Facebook na Dr. Ahmad Gumi. shahararren mai fafutukar kare hakkin ‘yan fashin daji bayan yayi suka ga maulidi a shafin a daidai lokacin da musulman suke  tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad SAWA.  A kowace shekara a cikin watan Rabi’ul Awwal, Musulmin duniya suna tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad ta hanyar karanta Alƙur’ani mai girma, ƙasidun yabo ya Annabi da karanta tarihin rayuwar sa. Shafin Dr. Gumi na Facebook ya samu sharhi sama da 600 har zuwa lokacin nan a tare da cewa suka yayi akan maulidin, amma da yawan su suna rubuta "Happy Maulud,"  duk da sun karanta sukar da yayi.   Karantarwar Dr Gumi tana fuskantar tsaiko da rashin tasiri akan mutane bayan ya karkatar da hankalin sa daga taimakon waɗanda rikicin yan fashin daji ya rutsa da su a arewa maso yammacin Najeriya zuwa neman haƙƙin masu aikata laifin.

PDP za ta 'Kwace mulki daga hannun APC a zaben 2023 - Inji Atiku Abubakar

Alh. Atiku Abubakar Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam'iyyar PDP, Mai adawa, za ta karbi mulki daga hannun jam'iyyar APC, mai mulki, a zaben shekarar 2023. Atku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a dandalin Mahmud Ribadu, Yola, wurin za'ben shugabannin  jam'iyyar PDP na jiha. Ya yi kira ga 'yan siyasa da su mutunta dokokin jam'iyya, na za'be, da Kuma na kundin tsarin mulkin kasar wajen zaben shugabannin jam'iyya, yana mai cewa dimokradiyya na iya 'dorewa ne a cikin yanayi na 'yanci da adalci

'Yan bindiga na karbar dafaffen abinci a matsayin kudin fansa a Jihar Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta dauki wasu tsauraran matakai domin yaki da 'yan bindiga.  Yanzu haka ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna sun bukaci a rika ba su dafaffen abinci a matsayin kudin fansa kafin sakin mutanen da suka yi garkuwa da su. Rahotanni na cewa, ‘yan bindigar sun janye daga kaddamar da hare-hare kan garuruwan jihar tun bayan da gwamnatin ta haramta cin kasuwannin mako-mako a wani bangare na daukar matakin magance matsalar tsaro. Daya daga cikin shugabannin matasan kauyukan Birnin Gwari Babangida Yaro ya shaida wa Jaridar Daily Trsut cewa, tun lokacin da gwamnati ta haramta cin kasuwannin, ‘yan bindigar ke neman a rika ba su dafaffen abinci a duk lokacin da suka sace mutun. Yaro ya kara da cewa, matakin hana sayar da man fetur a yankin, shi ma ya taimaka wajen takaita zirga-zairga. A cewarsa, an samu kwarya-kwaryar zaman lafiya a kauyukan Damari da Kuyello da Kutemashi saboda ‘yan bindigar sun daina kaddamar da farmaki, yayin da suka tare a...