Skip to main content

Wataƙila nan da shekara kuma ku fara hawa tasi mai tashi sama



Business reporter

Wani rahoto ya yi hasashen cewa daga nan zuwa shakerar 2040 za a samar da irin wannan mota guda 430,000 a faɗin duniya.

Da zarar aka yi batun tasi mai tashi sama don kai mutane anguwa a cikin gari, abin da ke fara zuwa zukatan wasu shi ne sanannen fim dinnan na zane wato 'The Jetsons'.

Cartoon din wanda aka yi a shekarar 1960 ya nuna wasu iyalai da ke rayuwa a wani gari na zamani, inda mutane ke zuwa aiki cikin wasu motoci da ke tashi sama.

Shekaru 20 a karni na 21, wasu masana kimiyya na kokarin mayar da mafarkin waɗanda suka shirya cartoon din Jetsons gaske.

A yanzu kamfanonin Uber da Boeing sun samar da motoci masu tashi sama.

Wani rahoto ma ya yi hasashen cewa daga nan zuwa shekarar 2040 za a samar da irin wadannan motoci guda 430,000 a faɗin duniya.

Wannan kuma na zuwa a dai dai lokacin da ake ci gaba da samar da jirage marasa matuki, da ake hasashen kasuwar su za ta bunkasa da fam biliyan hudu daga nan zuwa 2028.

To amma kafin a samu yadda ake so wurin wadatuwar waɗannan motoci da kuma jirage marasa matuki akwai bukatar birane su gina kananan tashoshin jirgi da masana suka saka wa suna "skysports".

Dole za a bukaci samar da waɗannan tashoshi don motocin hayar su samu wurin sauka don daukar mutane.

Kamfanin Joby Aviation na California a Amurka na gaba-gaba wurin samar da tasi mai tashi sama, don tuni ya gudanar da gwajin fiye da guda 1,000.

Kamfanin na fatan samun amincewar hukumar sufurin jiragen sama ta Amurka don fara aiki a shekarar 2024.

Motocin Joby za su iya daukar fasinjoji hudu, kuma za su iya tafiyar kilomita 322 a cikin awa ɗaya.

"Abin da muke so mu yi shi ne samar da wadatattun motoci a wuraren da ake bukatarsu," a cewar Oliver Walker, mai magana da yawun kamfanonin Joby.

"Muna aiki da hukumomi a birane don tabbatar da cewa an samar da tashoshin da waɗannan motoci za su rika yada zango."

"Abin da muke so mu yi shi ne samar da wadatattun motoci a wuraren da ake bukatarsu," a cewar Oliver Walker.

Joby ya hada hannu da kamfanin fasaha na Reef Technology, da nufin amfani da rufin garejin motocinsa.

Duk da shirin samar da motoci masu tashi sama ba magana ce ta yanzu-yanzu ba, batun na samun karɓuwa daga hukumomi a Amurka.

Tuni garuruwan Houston da Los Angeles da kuma Orlando suka fara shirin samar da tashoshin motoci masu tashi sama.

A cewar magajin garin Los Angeles Eric Garcetti, samar da motoci masu tashi a birane ba karamar nasara ba ce.

Amurkawa da dama na gani tsarin zai rage cunkoson ababen hawa a tituna kasar

A Birtaniya gwamnati ta yi maraba da shirin samar da tashar motoci masu tashi sama a kusa da wani filin kwallo da ke Coventry.

Sai dai masana sun bayyana cewa akwai kalubale da dama da suka yi tsayuwar gwamin jaki ga samar da tashohin motocin.

"Kafin a samu nasarar ganin waɗannan motoci sun yi aiki yadda aka gani a shirin Jetsons sai an shawo kan wasu matsalolin tun yanzu", a cewar Jennifer Ritchter, kwararriya kan jirage marasa matuki da kuma tasi mai tashi sama.

Wani gwaji kan yadda karamar tashar jirgi za ta kasance a birnin Coventry na Birtaniya

Aaaron Belbasis, masani kan harkokin fasahar zamani ya ce batun lafiya da kariya na da matukar muhimmanci a wannan batu."

Ya kara da cewa "idan har aka ce za a samu yawaitar motoci a sararin samaniya to akwai yiwuwar haɗari, ko kuma idan aka yi rashin sa'a mota ta fado babu shiri."

"Haka kuma idan mota ta fado ba wai wadanda ke ciki kawai za ta jikkata ba, har da wadanda za ta fado a kansu," a cewar Mr Belbasis.

An jima da yin gwajin jirgi marar matuki da ke isar da sako

Wasu masanan na ganin cewa akwai bukatar zuba jari wurin samar da tashoshi isassu ba wai a mayar da hankali wurin samar da motoci babu isassun filayen tashi da saukar su ba.

A cewar Ricky Sadhu duk da kalubalen da ke da akwai, akwai kuma haske ta ɓangaren bukata da sha'awar samar da tashoshin motoci masu tashi a biranen Amurka da Turai da kuma Asiya.

''Muna da burin ganin an samu tashoshi 200 a faɗin duniya cikin shekaru biyar,'' a cewar Sadhu, kuma duk da haka manyan birane za su bukaci fiye ma da haka.''
     

 BBC HAUSA ✍

Comments

Popular posts from this blog

Musulmai Sun Yi Martani Ga Gumi Bayan Sukar Da Yayi Akan Maulud

Musulman Najeriya sun mamaye shafin Facebook na Dr. Ahmad Gumi. shahararren mai fafutukar kare hakkin ‘yan fashin daji bayan yayi suka ga maulidi a shafin a daidai lokacin da musulman suke  tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad SAWA.  A kowace shekara a cikin watan Rabi’ul Awwal, Musulmin duniya suna tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad ta hanyar karanta Alƙur’ani mai girma, ƙasidun yabo ya Annabi da karanta tarihin rayuwar sa. Shafin Dr. Gumi na Facebook ya samu sharhi sama da 600 har zuwa lokacin nan a tare da cewa suka yayi akan maulidin, amma da yawan su suna rubuta "Happy Maulud,"  duk da sun karanta sukar da yayi.   Karantarwar Dr Gumi tana fuskantar tsaiko da rashin tasiri akan mutane bayan ya karkatar da hankalin sa daga taimakon waɗanda rikicin yan fashin daji ya rutsa da su a arewa maso yammacin Najeriya zuwa neman haƙƙin masu aikata laifin.

PDP za ta 'Kwace mulki daga hannun APC a zaben 2023 - Inji Atiku Abubakar

Alh. Atiku Abubakar Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam'iyyar PDP, Mai adawa, za ta karbi mulki daga hannun jam'iyyar APC, mai mulki, a zaben shekarar 2023. Atku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a dandalin Mahmud Ribadu, Yola, wurin za'ben shugabannin  jam'iyyar PDP na jiha. Ya yi kira ga 'yan siyasa da su mutunta dokokin jam'iyya, na za'be, da Kuma na kundin tsarin mulkin kasar wajen zaben shugabannin jam'iyya, yana mai cewa dimokradiyya na iya 'dorewa ne a cikin yanayi na 'yanci da adalci

'Yan bindiga na karbar dafaffen abinci a matsayin kudin fansa a Jihar Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta dauki wasu tsauraran matakai domin yaki da 'yan bindiga.  Yanzu haka ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna sun bukaci a rika ba su dafaffen abinci a matsayin kudin fansa kafin sakin mutanen da suka yi garkuwa da su. Rahotanni na cewa, ‘yan bindigar sun janye daga kaddamar da hare-hare kan garuruwan jihar tun bayan da gwamnatin ta haramta cin kasuwannin mako-mako a wani bangare na daukar matakin magance matsalar tsaro. Daya daga cikin shugabannin matasan kauyukan Birnin Gwari Babangida Yaro ya shaida wa Jaridar Daily Trsut cewa, tun lokacin da gwamnati ta haramta cin kasuwannin, ‘yan bindigar ke neman a rika ba su dafaffen abinci a duk lokacin da suka sace mutun. Yaro ya kara da cewa, matakin hana sayar da man fetur a yankin, shi ma ya taimaka wajen takaita zirga-zairga. A cewarsa, an samu kwarya-kwaryar zaman lafiya a kauyukan Damari da Kuyello da Kutemashi saboda ‘yan bindigar sun daina kaddamar da farmaki, yayin da suka tare a...