Skip to main content

HOTON SARKIN BUNGUDU BAYAN ALLAH YA KUBUTAR DA SHI.


Ga hoton Sarkin Bungudu (Sarkin Yanka Mai Daraja Ta Daya) nan ya na ta yawo a kafafen sadar da zumunta, bayan da Allah Ya kubutar da shi daga hannun masu garkuwa da mutane, wanda ya shafe tsawon kwanaki talatin da biyu (32) a hannunsu.
(1) Abu ne mai matukar tayar da hankali, a ce wadannan mutane har suna da karfin halin iya kama Sarki Mai Martaba ta daya, har suna da karfin ikon iya rike Sarki mai martaba ta daya tsawon lokaci, an kuma kasa bibiyarsu a amso shi.

(2) Wasu kafafun watsa labarai sun bayyana cewa ba a sako Sarkin Bungudu ba sai da aka biya kudin fansa kimanin naira miliyan ashirin (20,000,000) lakadan ba ajalan ba. (Vision FM, Farin Wata TV).

(3) Don Allah ku duba yanayin da Mai Martaba Sarki ya samu kansa a ciki, ku yi la'akari da yadda ya fita daga hayyacinsa!!! Duba hotunan nan nasa da ya ke cikin kayan alfarma na sarauta da kasaita, sannan ka duba hoton da aka dauka bayan samun kubutarsa.

A gaskiya dukkan wani nau'i na tashin hankali da barazana ya gama tabbata a Nigeria tuni!!! 

Lamarin wannan kasa ba abin wasa ba ne! Lamuran sun wuce dukkan yadda mutum ya ke sawwarawa Wallahi!

Ga mu ga Allah! Babu wayo babu dabara! Babu karfi babu iko! Babu mulki babu sarauta! Sai sallallami da salati.

Allah Ya jikan mu.

Comments

Popular posts from this blog

Musulmai Sun Yi Martani Ga Gumi Bayan Sukar Da Yayi Akan Maulud

Musulman Najeriya sun mamaye shafin Facebook na Dr. Ahmad Gumi. shahararren mai fafutukar kare hakkin ‘yan fashin daji bayan yayi suka ga maulidi a shafin a daidai lokacin da musulman suke  tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad SAWA.  A kowace shekara a cikin watan Rabi’ul Awwal, Musulmin duniya suna tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad ta hanyar karanta Alƙur’ani mai girma, ƙasidun yabo ya Annabi da karanta tarihin rayuwar sa. Shafin Dr. Gumi na Facebook ya samu sharhi sama da 600 har zuwa lokacin nan a tare da cewa suka yayi akan maulidin, amma da yawan su suna rubuta "Happy Maulud,"  duk da sun karanta sukar da yayi.   Karantarwar Dr Gumi tana fuskantar tsaiko da rashin tasiri akan mutane bayan ya karkatar da hankalin sa daga taimakon waɗanda rikicin yan fashin daji ya rutsa da su a arewa maso yammacin Najeriya zuwa neman haƙƙin masu aikata laifin.

PDP za ta 'Kwace mulki daga hannun APC a zaben 2023 - Inji Atiku Abubakar

Alh. Atiku Abubakar Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam'iyyar PDP, Mai adawa, za ta karbi mulki daga hannun jam'iyyar APC, mai mulki, a zaben shekarar 2023. Atku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a dandalin Mahmud Ribadu, Yola, wurin za'ben shugabannin  jam'iyyar PDP na jiha. Ya yi kira ga 'yan siyasa da su mutunta dokokin jam'iyya, na za'be, da Kuma na kundin tsarin mulkin kasar wajen zaben shugabannin jam'iyya, yana mai cewa dimokradiyya na iya 'dorewa ne a cikin yanayi na 'yanci da adalci

'Yan bindiga na karbar dafaffen abinci a matsayin kudin fansa a Jihar Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta dauki wasu tsauraran matakai domin yaki da 'yan bindiga.  Yanzu haka ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna sun bukaci a rika ba su dafaffen abinci a matsayin kudin fansa kafin sakin mutanen da suka yi garkuwa da su. Rahotanni na cewa, ‘yan bindigar sun janye daga kaddamar da hare-hare kan garuruwan jihar tun bayan da gwamnatin ta haramta cin kasuwannin mako-mako a wani bangare na daukar matakin magance matsalar tsaro. Daya daga cikin shugabannin matasan kauyukan Birnin Gwari Babangida Yaro ya shaida wa Jaridar Daily Trsut cewa, tun lokacin da gwamnati ta haramta cin kasuwannin, ‘yan bindigar ke neman a rika ba su dafaffen abinci a duk lokacin da suka sace mutun. Yaro ya kara da cewa, matakin hana sayar da man fetur a yankin, shi ma ya taimaka wajen takaita zirga-zairga. A cewarsa, an samu kwarya-kwaryar zaman lafiya a kauyukan Damari da Kuyello da Kutemashi saboda ‘yan bindigar sun daina kaddamar da farmaki, yayin da suka tare a...