Skip to main content

Tabbas zan iya komawa APC, Kwankwaso

Tabbas Zan Koma Jam,iyar APC Idan Har Akamin Alkawarin Kujerar Mataimakin Shugaban Kasa Azaben 2023, Cewar Kwankwaso. 

Wato jama,a yanzu haka majiyar mu ta labarta mana cewa tsohon gwamnan jihar kano sanata rabi,u musa kwankwaso yama jam,iyar APC albishir da cewa idan har jam,iyar tamai alkawarin mataimakin shugaban kasa 2023 tare da masa alkawarin barin tafiyar kwankwasiya a cikin Nijeriya babu shekka zai koma jam,iyar ta APC.

Kamar yadda muka samu labarin cewa sabbin rahotanni sun fito game da shirin tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso na komawa APC

Wasu majiyoyi masu ƙarfi sun bayyana cewa Kwankwaso ya kafa wa wakilan APC wasu sharuɗɗa kafin ya koma jam'iyyar ta APC

Kamar yadda wata majiya ta sheda mana cewa tun bayan kammala wa'adin mulkin Kwankwaso da Ganduje a 2015, har yanzu Ganduje da Kwankwaso wanda suka kasance abokan juna basa shiri amma ana kyautata zatan zasu shirya gabanin babban zaben 2023

Rahotanni sun bayyana wasu dalilai da yasa har zuwa yanzun tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso, bai koma APC ba didda bukatar da yake da ita a siyasan ce. 

Wata majiya mai ƙarfi ta shaidawa Leadership cewa Kwankwaso na fatan tsira da mutuncinsa kuma ya kafa wa APC wasu sharuɗɗa na shiga jam'iyyar.

Kasancewar ana ta cece-kuce kuma shugabannin Arewa na ganin ya kamata a baiwa kudu takarar shugaban ƙasa a 2023, Kwankwaso ya kafawa APC sharaɗin cewa za'a ba shi kujerar mataimaki a 2023 idan har ana so yakuma jam,iyar ta APC.

Haka kuma Kwankwaso ya shaidawa APC cewa ba za'a yi karambanin ruguza tafiyarsa ta Kwankwasiyya ba a faɗin Nijeriya.

Bugu da kari, Kwankwaso ya bukaci a miƙa masa ragamar jagorancin APC a Kano, maimakon gwamna Ganduje, wanda ya kasance mataimakinsa a baya. 

Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa ba'a ga maciji tsakanin Kwankwaso da Ganduje tun bayan ƙarewar wa'adin mulkinsu a shekarar 2015. 

Masu karatu ya kuke kallan kumawar kwankwaso jam,iyar APC.?

Comments

Popular posts from this blog

Musulmai Sun Yi Martani Ga Gumi Bayan Sukar Da Yayi Akan Maulud

Musulman Najeriya sun mamaye shafin Facebook na Dr. Ahmad Gumi. shahararren mai fafutukar kare hakkin ‘yan fashin daji bayan yayi suka ga maulidi a shafin a daidai lokacin da musulman suke  tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad SAWA.  A kowace shekara a cikin watan Rabi’ul Awwal, Musulmin duniya suna tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad ta hanyar karanta Alƙur’ani mai girma, ƙasidun yabo ya Annabi da karanta tarihin rayuwar sa. Shafin Dr. Gumi na Facebook ya samu sharhi sama da 600 har zuwa lokacin nan a tare da cewa suka yayi akan maulidin, amma da yawan su suna rubuta "Happy Maulud,"  duk da sun karanta sukar da yayi.   Karantarwar Dr Gumi tana fuskantar tsaiko da rashin tasiri akan mutane bayan ya karkatar da hankalin sa daga taimakon waɗanda rikicin yan fashin daji ya rutsa da su a arewa maso yammacin Najeriya zuwa neman haƙƙin masu aikata laifin.

PDP za ta 'Kwace mulki daga hannun APC a zaben 2023 - Inji Atiku Abubakar

Alh. Atiku Abubakar Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam'iyyar PDP, Mai adawa, za ta karbi mulki daga hannun jam'iyyar APC, mai mulki, a zaben shekarar 2023. Atku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a dandalin Mahmud Ribadu, Yola, wurin za'ben shugabannin  jam'iyyar PDP na jiha. Ya yi kira ga 'yan siyasa da su mutunta dokokin jam'iyya, na za'be, da Kuma na kundin tsarin mulkin kasar wajen zaben shugabannin jam'iyya, yana mai cewa dimokradiyya na iya 'dorewa ne a cikin yanayi na 'yanci da adalci

'Yan bindiga na karbar dafaffen abinci a matsayin kudin fansa a Jihar Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta dauki wasu tsauraran matakai domin yaki da 'yan bindiga.  Yanzu haka ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna sun bukaci a rika ba su dafaffen abinci a matsayin kudin fansa kafin sakin mutanen da suka yi garkuwa da su. Rahotanni na cewa, ‘yan bindigar sun janye daga kaddamar da hare-hare kan garuruwan jihar tun bayan da gwamnatin ta haramta cin kasuwannin mako-mako a wani bangare na daukar matakin magance matsalar tsaro. Daya daga cikin shugabannin matasan kauyukan Birnin Gwari Babangida Yaro ya shaida wa Jaridar Daily Trsut cewa, tun lokacin da gwamnati ta haramta cin kasuwannin, ‘yan bindigar ke neman a rika ba su dafaffen abinci a duk lokacin da suka sace mutun. Yaro ya kara da cewa, matakin hana sayar da man fetur a yankin, shi ma ya taimaka wajen takaita zirga-zairga. A cewarsa, an samu kwarya-kwaryar zaman lafiya a kauyukan Damari da Kuyello da Kutemashi saboda ‘yan bindigar sun daina kaddamar da farmaki, yayin da suka tare a...