Skip to main content

Jam'iyyar APC zata wargaje a Kano. Inji Shekarau


    Sen. Mal. Ibrahim Shekarau

Sakamakon rikicin da ya barke a jam'iyyar APC, Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta kira taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar

Gwamna Ganduje ya karanto sunayen mutanen da Gwamnatin Kano ta basu mukamai na jam'iyya a matakin jiha wanda zata tabbatar dasu gobe Asabar idan Allah Ya kaimh

A wajen taron da ya gabata jiya, Gwamna Ganduje ya keta alfarmar tsohon Gwamnan jihar Kano, kuma Sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano) inda ya kirashi da:
-Makaryaci
-Mai karbe-karbe
-Banza Bakwai

Hakika Gwamna Ganduje ya tafka babban kuskure da ya karbi shawaran miyagun da suke jikinsa har yake ganin zai iya ja da Malam Ibrahim Shekarau ya kai labari

A jihar Kano, bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso babu wanda ya kai Malam Ibrahim Shekarau yawan masoya mabiya, nima Datti Assalafiy a dalilin Malam Ibrahim Shekarau na shigo yabon Gwamna Ganduje

Kuma na tabbata imba don Malam Ibrahim Shekarau ya zama sanadi ba, Wallahi zaben 2019 ba inda Gwamna Ganduje zai je, da bai kai labari ba, tabbas bai kamata a yiwa Malam Ibrahim Shekarau butulci ba

Lallai duk inda Malam Ibrahim Shekarau ya nufa zamu bishi, kuma muna tare dashi a kowace jam'iyya na siyasa

Allah Ka daukaka darajar Malam Ibrahim Shekarau

Zubin rubutu: Salisu Idris Waziri

Comments

Popular posts from this blog

Musulmai Sun Yi Martani Ga Gumi Bayan Sukar Da Yayi Akan Maulud

Musulman Najeriya sun mamaye shafin Facebook na Dr. Ahmad Gumi. shahararren mai fafutukar kare hakkin ‘yan fashin daji bayan yayi suka ga maulidi a shafin a daidai lokacin da musulman suke  tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad SAWA.  A kowace shekara a cikin watan Rabi’ul Awwal, Musulmin duniya suna tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad ta hanyar karanta Alƙur’ani mai girma, ƙasidun yabo ya Annabi da karanta tarihin rayuwar sa. Shafin Dr. Gumi na Facebook ya samu sharhi sama da 600 har zuwa lokacin nan a tare da cewa suka yayi akan maulidin, amma da yawan su suna rubuta "Happy Maulud,"  duk da sun karanta sukar da yayi.   Karantarwar Dr Gumi tana fuskantar tsaiko da rashin tasiri akan mutane bayan ya karkatar da hankalin sa daga taimakon waɗanda rikicin yan fashin daji ya rutsa da su a arewa maso yammacin Najeriya zuwa neman haƙƙin masu aikata laifin.

PDP za ta 'Kwace mulki daga hannun APC a zaben 2023 - Inji Atiku Abubakar

Alh. Atiku Abubakar Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam'iyyar PDP, Mai adawa, za ta karbi mulki daga hannun jam'iyyar APC, mai mulki, a zaben shekarar 2023. Atku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a dandalin Mahmud Ribadu, Yola, wurin za'ben shugabannin  jam'iyyar PDP na jiha. Ya yi kira ga 'yan siyasa da su mutunta dokokin jam'iyya, na za'be, da Kuma na kundin tsarin mulkin kasar wajen zaben shugabannin jam'iyya, yana mai cewa dimokradiyya na iya 'dorewa ne a cikin yanayi na 'yanci da adalci

'Yan bindiga na karbar dafaffen abinci a matsayin kudin fansa a Jihar Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta dauki wasu tsauraran matakai domin yaki da 'yan bindiga.  Yanzu haka ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna sun bukaci a rika ba su dafaffen abinci a matsayin kudin fansa kafin sakin mutanen da suka yi garkuwa da su. Rahotanni na cewa, ‘yan bindigar sun janye daga kaddamar da hare-hare kan garuruwan jihar tun bayan da gwamnatin ta haramta cin kasuwannin mako-mako a wani bangare na daukar matakin magance matsalar tsaro. Daya daga cikin shugabannin matasan kauyukan Birnin Gwari Babangida Yaro ya shaida wa Jaridar Daily Trsut cewa, tun lokacin da gwamnati ta haramta cin kasuwannin, ‘yan bindigar ke neman a rika ba su dafaffen abinci a duk lokacin da suka sace mutun. Yaro ya kara da cewa, matakin hana sayar da man fetur a yankin, shi ma ya taimaka wajen takaita zirga-zairga. A cewarsa, an samu kwarya-kwaryar zaman lafiya a kauyukan Damari da Kuyello da Kutemashi saboda ‘yan bindigar sun daina kaddamar da farmaki, yayin da suka tare a...