Skip to main content

Jerin sunayen 'yan Nigeria 11 da aka kama a Amurka kan almundahanar kudi da damfarar mutane fiye da 50


An kama wasu 'yan Nigeria 11 a Amurka bisa laifuka na almundahar kudade Laifukan da suka aikata sun hada da damfarar kamfanoni da mutane ta hanyar soyayya Masu bincike sun ce za a gurfanar da su a kotu domin su girbi abin da suka shuka, Hukumar binciken shari'a na Amurka ya gurfanar da wasu 'yan Nigeria 11 a kotu kan zarginsu da hada baki wurin aikata almundahar kudade, damfara ta banki da satar kudade da sunan wasu. A ranar Laraba ne Attoni na Kudancin New York, Damian Williams da Jam'in FBI mai kula da New York, Patrick J, Freancy suka sanar da sunayen 'yan Nigeria 11 da ke da hannu wurin karkatar da miliyoyin daloli daga damfarar imel da damfarar soyayya. 


EFCC Ta Gurfanar Da Yarima Gaban Kotu
EFCC ta gurfanar da Yarima a gaban kotu kan badakalar N35.5m 'Yan Nigeria 11 da aka gurfanar a Amurka kan almundahar kudi da damfarar mutane fiye da 50.

Hukumar binciken shari'a na Amurka ta bayyana hakan a ranar Laraba kamar yadda ya zo a ruwayar SaharaReporters.

An kama mutum tara cikinsu a New Jersey da Gabashin New York kuma za a gurfanar da su gaban Mai shari'a Sarah Netburn a Kudanci New York. Daya daga cikin wadanda ake zargin an kama shi ne a kudancin Texas kuma za a masa shari'a a kotun tarayya na yankin. Daya kuma har yanzu ana nemansa.

 Jerin sunayensu Wadanda ake zargi da almundahar kudin sune: 

1 Adedayo John 
2 Oluwadamilola Akinpelu
3 Kazeem Raheem 
4 Morakinyo Gbeyide 
5 Warris Adenuga, a.k.a 'Blue' 
6 Smart Agunbiade 
7 Lateef Goloba
8 Samsondeen Goloba 
9Olawale Olaniyan
0 Olawoyin Peter Olarewaju, da
1 Emmanuel Oronsaye-Ajayi 

An ruwaito Williams na cewa: 

"Kamar yadda ake tuhumarsu, wadanda aka kama suna cikin wata kungiyar bata gari da ke damfarar kamfanoni a intanet sannan suna damfarar dattawa ta hanyar yaudarar su da soyayya suna tura musu kudade, godiya ga 'yan sandan sirri na Secret Service, yanzu wadanda ake tuhuma suna kotu.

 Duk da komawa APC, da alamu Fani-Kayode zai fuskanci fushin kotu saboda badakala Freaney ya ce 'yan sandan na Secret Service za su cigaba da kare 'yan Amurka daga barazanar 'yan damfara masu yi wa kudadensu barazana kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

'Yan Sanda Sunyi Ram Da Wani Sojan Gona
 ‘Yan sanda sun yi ram da wani sojan bogi, mai yi wa mata sata da sunan zai aure su A wani rahoton, ‘yan sanda sun kama Mkwatula mai shekaru 38 bisa yi wa tarin mata sata bayan dankara mu su karyar shi sojan Malawi ne kuma auren su ze yi bisa ruwayar LIB.

 Kakakin rundunar ‘yan sandan Ntcheu, Rabecca Kwisongole ta ce wanda ake zargin ya dade ya na yaudarar mata da soyayya da kuma alkawarin auren su. A cewar Kwisongole, bayan kwanaki da mika tayin soyayyar sa ga mace, Mkwatula zai lallaba ya sace mu su abubuwa masu daraja kamar babura, talabijin, wayoyi, barguna har kudade ma. 

Source: Legit.ng News

Comments

Popular posts from this blog

Musulmai Sun Yi Martani Ga Gumi Bayan Sukar Da Yayi Akan Maulud

Musulman Najeriya sun mamaye shafin Facebook na Dr. Ahmad Gumi. shahararren mai fafutukar kare hakkin ‘yan fashin daji bayan yayi suka ga maulidi a shafin a daidai lokacin da musulman suke  tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad SAWA.  A kowace shekara a cikin watan Rabi’ul Awwal, Musulmin duniya suna tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad ta hanyar karanta Alƙur’ani mai girma, ƙasidun yabo ya Annabi da karanta tarihin rayuwar sa. Shafin Dr. Gumi na Facebook ya samu sharhi sama da 600 har zuwa lokacin nan a tare da cewa suka yayi akan maulidin, amma da yawan su suna rubuta "Happy Maulud,"  duk da sun karanta sukar da yayi.   Karantarwar Dr Gumi tana fuskantar tsaiko da rashin tasiri akan mutane bayan ya karkatar da hankalin sa daga taimakon waɗanda rikicin yan fashin daji ya rutsa da su a arewa maso yammacin Najeriya zuwa neman haƙƙin masu aikata laifin.

PDP za ta 'Kwace mulki daga hannun APC a zaben 2023 - Inji Atiku Abubakar

Alh. Atiku Abubakar Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam'iyyar PDP, Mai adawa, za ta karbi mulki daga hannun jam'iyyar APC, mai mulki, a zaben shekarar 2023. Atku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a dandalin Mahmud Ribadu, Yola, wurin za'ben shugabannin  jam'iyyar PDP na jiha. Ya yi kira ga 'yan siyasa da su mutunta dokokin jam'iyya, na za'be, da Kuma na kundin tsarin mulkin kasar wajen zaben shugabannin jam'iyya, yana mai cewa dimokradiyya na iya 'dorewa ne a cikin yanayi na 'yanci da adalci

'Yan bindiga na karbar dafaffen abinci a matsayin kudin fansa a Jihar Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta dauki wasu tsauraran matakai domin yaki da 'yan bindiga.  Yanzu haka ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna sun bukaci a rika ba su dafaffen abinci a matsayin kudin fansa kafin sakin mutanen da suka yi garkuwa da su. Rahotanni na cewa, ‘yan bindigar sun janye daga kaddamar da hare-hare kan garuruwan jihar tun bayan da gwamnatin ta haramta cin kasuwannin mako-mako a wani bangare na daukar matakin magance matsalar tsaro. Daya daga cikin shugabannin matasan kauyukan Birnin Gwari Babangida Yaro ya shaida wa Jaridar Daily Trsut cewa, tun lokacin da gwamnati ta haramta cin kasuwannin, ‘yan bindigar ke neman a rika ba su dafaffen abinci a duk lokacin da suka sace mutun. Yaro ya kara da cewa, matakin hana sayar da man fetur a yankin, shi ma ya taimaka wajen takaita zirga-zairga. A cewarsa, an samu kwarya-kwaryar zaman lafiya a kauyukan Damari da Kuyello da Kutemashi saboda ‘yan bindigar sun daina kaddamar da farmaki, yayin da suka tare a...