Skip to main content

'Yan bindiga na karbar dafaffen abinci a matsayin kudin fansa a Jihar Kaduna


Gwamnatin Kaduna ta dauki wasu tsauraran matakai domin yaki da 'yan bindiga. 

Yanzu haka ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna sun bukaci a rika ba su dafaffen abinci a matsayin kudin fansa kafin sakin mutanen da suka yi garkuwa da su.

Rahotanni na cewa, ‘yan bindigar sun janye daga kaddamar da hare-hare kan garuruwan jihar tun bayan da gwamnatin ta haramta cin kasuwannin mako-mako a wani bangare na daukar matakin magance matsalar tsaro.

Daya daga cikin shugabannin matasan kauyukan Birnin Gwari Babangida Yaro ya shaida wa Jaridar Daily Trsut cewa, tun lokacin da gwamnati ta haramta cin kasuwannin, ‘yan bindigar ke neman a rika ba su dafaffen abinci a duk lokacin da suka sace mutun.

Yaro ya kara da cewa, matakin hana sayar da man fetur a yankin, shi ma ya taimaka wajen takaita zirga-zairga.

A cewarsa, an samu kwarya-kwaryar zaman lafiya a kauyukan Damari da Kuyello da Kutemashi saboda ‘yan bindigar sun daina kaddamar da farmaki, yayin da suka tare a daji suna kwace dafaffen abinci hatta daga hannun masu sayar da abinci.

Har ila yau, Yaro ya kara da cewa, a duk lokacin da ‘yan bindigar suka sace mutune biyu zuwa uku a gona, suna barin mutun guda domin karbo musu abinci daga hannun iyalan wadanda aka yi garkuwa da su a matsayin fansa, la’akari da cewa, babu hanyar sadarwar wayoyin hannu da aka katse.

Comments

Popular posts from this blog

An Cafke Malamar Makarantar Da Ta Yiwa Yaro Ɗan Shekara 15 Fyaɗe

Wannan itace matar da hukumar 'yan sanda ke tuhuma da yiwa wani yaro Fyade. Bambarakwai, wai namiji da sunan Hajara,  Duk da Tuhumar da jami'ai ke yiwa matar, a bangare guda *yaron ya bayyana cewa ba fyaɗe ta mishi ba, da son rainsa suka yi lalata. An kama matar ne dauke da ciki niki-niki bayan da tawa wani ƙaramin yaro dan shekaru 15 fyaɗe. Matar mai suna Heiry Calvi dake karantarwa a makaranta dake Florida ta ƙasar Amurka na fuskantar tuhumar cin zarafin ƙaramin yaro. Sai dai yaron yace ba fyaɗe ta masa ba, da son ransa suka yi lalatar, amma an sanar da shi cewa doka bata yarda da hakan ba, har sai ya kai shekaru 18. An dai kasa tantance cikin na wanene, amma dai ƴan sanda sun kama matar suna bincike. Mu dai anan sadai muce... Can ga su Gada, Wai Zomo yaji kidan 'yan farauta.

Ganduje ya bai wa makaho aiki saboda bajintarsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bai wa Ɗahuru Abdulhamid Idris wanda makaho ne, aikin koyarwa a gwamnatin jihar. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Sakataren Labarai na gwamnatin jihar, Abba Anwar ya fitar a ranar Lahadi. Kafin wannan lokaci, Ɗahuru ya kasance yana aikin koyarwa na sa-kai ba tare da ana biyansa wani albashi ba. Sanarwar ta ce bayan da Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Muhammadu Sanusi Kiru, ya jagoranci Ɗahuru zuwa gaban Ganduje ne, a nan Ganduje ya bada umarnin a ɗauke shi aiki sannan a tura shi Makarantar Nakasassu da ke Tudun Maliki don ya ci gaba koyarwa. Yayin ganawar tasu, Ganduje ya yaba wa ƙoƙarin Ɗahuru musamman ma ganin yadda bai bari lalurar makanta ta hana shi bada tasa gudunmawa ga cigaban fannin ilimin jihar ba. Bisa wannan dalili ne Gwamna Ganduje ya ce, “Lallai ka taki matakin da ya dace a rayuwarka. Gwamnatin jihar Kano ta ba ka aikin koyarwa. Kuma na umarci Kwamishinan Ilimi da a tura ka zu...

Kamfanin Facebook Zai Canza Sunan Sa.

LABARU DA DUMI-DUMIN SU! Shahararren dandalin sada zumunta na Facebook Inc yana shirin sake sunan kansa da sabon suna a mako mai zuwa, shafin yanar gizo na fasahar Amurka Verge ya ruwaito a ranar Talata, inda ya ambaci wata majiya da ke da masaniya kai tsaye kan lamarin.  Babban Jami'i kuma Shugaban Facebook Mark Zuckerberg yana shirin yin magana game da canjin sunan a taron haɗin gwiwa na kamfani na shekara -shekara a ranar 28 ga Oktoba, amma ana iya bayyana shi da wuri, inji rahoton Verge. Labarin na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin ke fuskantar karuwar sanya ido daga gwamnati a Amurka kan harkokin kasuwancinsa.  Sake canza sunan zai sanya aikace -aikacen kafofin watsa labarun Facebook a matsayin ɗayan samfura da yawa a ƙarƙashin kamfanin, wanda kuma zai kula da sauran manhajojin sa kamar Instagram, WhatsApp, Oculus da sauran su, in ji rahoton Verge.  Ba sabon abu bane a Silicon Valley don kamfanoni sun canza sunayensu yayin da suke neman fadada ayyukan ...