Skip to main content

Gwamnatin Kaduna ta ce an kashe mutum 343 cikin wata uku a jihar



Daga: Comrade Musa Garba Augie.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum 343 sakamakon ayyukan 'yan fashin daji da sauran tashe-tashen hankali cikin wata uku.

Cikin wani rahoto da ya fitar ranar Laraba, Kwamashinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa 'yan bindigar da ake zaton 'yan fashin daji ne sun sace mutum 830 a watannin.

Rahoton ya duba rikice-rikicen da suka faru ne daga 1 ga watan Yuli zuwa 30 ga Satumban 2021.

Sai dai rahoton ya nuna cewa adadin waɗanda aka sace a wata ukun ya ƙaru a kan na watannin Afrilu zuwa Yuni, inda aka sace 774 kuma aka kashe 222.

•Na cire ɗana daga makarantar gwamnati saboda 'yan fashi na ƙoƙarin sace shi - El-Rufai
•'Yan bindiga sun kai hari Makarantar Sojoji ta NDA
•Abin da ya sa El-Rufai ba ya goyon bayan yin sulhu da ƴan bindiga
•A gefe guda kuma, Mista Aruwan ya ce jami'an tsaro sun kashe jumillar 'yan fashi 69 a wurare daba-daban na jihar tare da tarwatsa sansanoninsu.

Daga cikin waɗanda aka sace ɗin, Mazaɓar Sanatan Kaduna ta Tsakiya ce ke da 732 bayan an ɗqauke su a ƙananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa da Igabi da Chikun da Kajuru. Sai Mazaɓar Kudancin Kaduna da ke biye mata da mutum 51 da kuma Arewaci mai 41.

Kazalika, Kudancin Kaduna ne ke da mafi yawan mutanen da suka mutu da mutum 193, Mazaɓar Tsakiya na da 130 da kuma Arewaci da ke da mutum 20.

Haka nan, an sace dabbobin da suka haɗa da shanu da akuyoyi da tunkiyoyi har 1,018 cikin wata ukun, yayin da aka sace 780 a Mazaɓar Kaduna ta Tsakiya.

Kwamashina Aruwan ya ce rikice-rikicen sun jikkata mutum 210 jumilla.

A watan Satumba ne wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriya suka ɗauki matakin toshe layukan sadarwa ciki har da Kaduna da zummar daƙile ayyukan 'yan fashin.


Comments

Popular posts from this blog

EFCC ta ƙaddamar da sabon salon yaƙi da rashawa a Najeriya

Shugaban EFCC Abdurrashid  Bawa Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya ce hukumar za ta fifita daƙile aikata laifuka kafin a aikata su Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta ce ta ɓullo da wani sabon salon daƙile ayyukan rashawa, inda za ta fi mayar da hankali kan rigakafin daƙile laifin kafin a aikata shi. A cewar Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa, daga yanzu hukumar za ta fi mayar da hankali wajen haɗa kai da abokan hulɗarta musamman na ƙasashen waje domin yaƙi da ayyukan rashawa. Da yake magana yayin taron ƙaddamar da sabon tsarin aikin a Abuja, Abdulrasheed Bawa ya ce sabon tsarin na 2021 zuwa 2025 an ciro shi ne daga kundin muradai na EFCC na shekarar 2013 zuwa 2018. "Sabon salon ya fi fifita rigakafi (hana faruwar laifi) a matsayin hanya mafi sauƙin daƙile rashawa fiye da yin hukunci," a cewarsa kamar yadda mujallar EFCC ta mako-mako ta ruwaito. Ya ƙara da cewa sabon tsarin zai fifita tattara bayanan sirri da gurfanar da masu laifi a gaban kotu...

Ganduje ya bai wa makaho aiki saboda bajintarsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bai wa Ɗahuru Abdulhamid Idris wanda makaho ne, aikin koyarwa a gwamnatin jihar. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Sakataren Labarai na gwamnatin jihar, Abba Anwar ya fitar a ranar Lahadi. Kafin wannan lokaci, Ɗahuru ya kasance yana aikin koyarwa na sa-kai ba tare da ana biyansa wani albashi ba. Sanarwar ta ce bayan da Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Muhammadu Sanusi Kiru, ya jagoranci Ɗahuru zuwa gaban Ganduje ne, a nan Ganduje ya bada umarnin a ɗauke shi aiki sannan a tura shi Makarantar Nakasassu da ke Tudun Maliki don ya ci gaba koyarwa. Yayin ganawar tasu, Ganduje ya yaba wa ƙoƙarin Ɗahuru musamman ma ganin yadda bai bari lalurar makanta ta hana shi bada tasa gudunmawa ga cigaban fannin ilimin jihar ba. Bisa wannan dalili ne Gwamna Ganduje ya ce, “Lallai ka taki matakin da ya dace a rayuwarka. Gwamnatin jihar Kano ta ba ka aikin koyarwa. Kuma na umarci Kwamishinan Ilimi da a tura ka zu...

PDP za ta 'Kwace mulki daga hannun APC a zaben 2023 - Inji Atiku Abubakar

Alh. Atiku Abubakar Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam'iyyar PDP, Mai adawa, za ta karbi mulki daga hannun jam'iyyar APC, mai mulki, a zaben shekarar 2023. Atku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a dandalin Mahmud Ribadu, Yola, wurin za'ben shugabannin  jam'iyyar PDP na jiha. Ya yi kira ga 'yan siyasa da su mutunta dokokin jam'iyya, na za'be, da Kuma na kundin tsarin mulkin kasar wajen zaben shugabannin jam'iyya, yana mai cewa dimokradiyya na iya 'dorewa ne a cikin yanayi na 'yanci da adalci