Shugaban EFCC Abdurrashid Bawa Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya ce hukumar za ta fifita daƙile aikata laifuka kafin a aikata su Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta ce ta ɓullo da wani sabon salon daƙile ayyukan rashawa, inda za ta fi mayar da hankali kan rigakafin daƙile laifin kafin a aikata shi. A cewar Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa, daga yanzu hukumar za ta fi mayar da hankali wajen haɗa kai da abokan hulɗarta musamman na ƙasashen waje domin yaƙi da ayyukan rashawa. Da yake magana yayin taron ƙaddamar da sabon tsarin aikin a Abuja, Abdulrasheed Bawa ya ce sabon tsarin na 2021 zuwa 2025 an ciro shi ne daga kundin muradai na EFCC na shekarar 2013 zuwa 2018. "Sabon salon ya fi fifita rigakafi (hana faruwar laifi) a matsayin hanya mafi sauƙin daƙile rashawa fiye da yin hukunci," a cewarsa kamar yadda mujallar EFCC ta mako-mako ta ruwaito. Ya ƙara da cewa sabon tsarin zai fifita tattara bayanan sirri da gurfanar da masu laifi a gaban kotu...
Labarai Da-Duminsu