Skip to main content

Ganduje ya bai wa makaho aiki saboda bajintarsa




Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bai wa Ɗahuru Abdulhamid Idris wanda makaho ne, aikin koyarwa a gwamnatin jihar.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Sakataren Labarai na gwamnatin jihar, Abba Anwar ya fitar a ranar Lahadi.

Kafin wannan lokaci, Ɗahuru ya kasance yana aikin koyarwa na sa-kai ba tare da ana biyansa wani albashi ba.

Sanarwar ta ce bayan da Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Muhammadu Sanusi Kiru, ya jagoranci Ɗahuru zuwa gaban Ganduje ne, a nan Ganduje ya bada umarnin a ɗauke shi aiki sannan a tura shi Makarantar Nakasassu da ke Tudun Maliki don ya ci gaba koyarwa.

Yayin ganawar tasu, Ganduje ya yaba wa ƙoƙarin Ɗahuru musamman ma ganin yadda bai bari lalurar makanta ta hana shi bada tasa gudunmawa ga cigaban fannin ilimin jihar ba.

Bisa wannan dalili ne Gwamna Ganduje ya ce, “Lallai ka taki matakin da ya dace a rayuwarka. Gwamnatin jihar Kano ta ba ka aikin koyarwa. Kuma na umarci Kwamishinan Ilimi da a tura ka zuwa makarantar masu fama da nakasa da ke Tudun Maliki.”

Yanzu dai ya tabbata cewa, Ɗahuru Andulhami Idiris ya zama ma’aikacin gwamnatin jihar Kano inda ake sa ran shi ma ya riƙa cin albashi kamar sauran ma’aikatan jihar duk ƙarshen wata.

ZangonLabarai

Comments

Popular posts from this blog

Buhari ya fusata da kisar gillar da aka yi wa masu cin kasuwa a garin Goronyo dake gabashin jihar Sokoto.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi matukar fusata da kisan gillar da aka yi wa masu cin Kasuwa a Goronyo, Jihar Sokoto inda ya aika wa ƴan bindiga sakon ‘Ta su ta kare’ ranar Litinin. Kakakin fadar shugaban ƙasa, Garba Shehu a wata takarda daga fadar shugaba Buhari ranar Litinin ya bayyana cewa shugaban Buhari ya fusata matuka da kisan da aka yi wa ƴan kasuwa da basu ji ba basu gani ba a kasuwar goronyo. Buhari ya ce wannan karon ƴan bindigan sun kai gwamnati maƙura kuma sun siya da kuɗin su domin sai sun gwammace kiɗa da karatu nan ba da daɗewa ba. ” Ko a yanzu ba su ji da daɗi daga dakarun Najeriya ta sama da kasa ba. Hakan yasa suke bin mutanen da basu ji ba basu gani suna kashe su. Wannan abu ya kai mu makura yanzu kuma lallai su kwana da shirin ta su ta kare. Harin Goronyo A kasuwar Goronyo jihar Sokoto dake ci mako-mako ne ‘yan bindiga suka buda wa mutane wuta inda suka kashe mutum sama da 30 sannan da dama sun ji rauni. Wannan hari ya auku ne kwanaki 12 da wasu ‘ya

Gwamnatin Kaduna ta ce an kashe mutum 343 cikin wata uku a jihar

Daga: Comrade Musa Garba Augie. Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum 343 sakamakon ayyukan 'yan fashin daji da sauran tashe-tashen hankali cikin wata uku. Cikin wani rahoto da ya fitar ranar Laraba, Kwamashinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa 'yan bindigar da ake zaton 'yan fashin daji ne sun sace mutum 830 a watannin. Rahoton ya duba rikice-rikicen da suka faru ne daga 1 ga watan Yuli zuwa 30 ga Satumban 2021. Sai dai rahoton ya nuna cewa adadin waɗanda aka sace a wata ukun ya ƙaru a kan na watannin Afrilu zuwa Yuni, inda aka sace 774 kuma aka kashe 222. •Na cire ɗana daga makarantar gwamnati saboda 'yan fashi na ƙoƙarin sace shi - El-Rufai •'Yan bindiga sun kai hari Makarantar Sojoji ta NDA •Abin da ya sa El-Rufai ba ya goyon bayan yin sulhu da ƴan bindiga •A gefe guda kuma, Mista Aruwan ya ce jami'an tsaro sun kashe jumillar 'yan fashi 69 a wurare daba-daban na jihar tare da tarwatsa sansanon

Sokoto: 'Ƴan bindiga sun kashe mutum 49 a kasuwar Goronyo'

Tambuwal Rahotanni daga jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya na cewa ƴan bidnga sun kashe aƙalla mutum 49 a wata kasuwa a garin Goronyo na jihar. Wasu ganau sun tabbatar wa da BBC labarin inda suka ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da yamma, yayin da mutanen ke cin babbar kasuwar Goronyon. Mutanen waɗanda suka buƙaci a sakaya sunayensu saboda tsaro sun ce ƴan bindigar sun afka wa kasuwar ne a yayin da ta cika makil da masu hada-hada daga sassan jihar da ma wasu yankunan. "Ƴan fashin sun zo ne da misalin ƙarfe 4.30 zuwa biyar na yamma suka zagaye kasuwar suka buɗe wuta ta kowane ɓangare," in ji ganau ɗin. Majiyarmu ta yi ƙoƙarin jin ta bakin rund8nar ƴan sanda jihar, amma ba mu samu mai magana da yawun ƴan sanda ba a kiran waya da aka yi ta yi masa. Ya ƙara da cewa "Mutane duk suka ruɗe wasu sun kwakkwanta a ƙasa don gudun harbin ya same su, yayin da wasu suka gudu amma masu tsautsayi sun rasa rayukansu." Ganau ɗin sun ce an ƙidaya gawa 49 yayin