Skip to main content

Sokoto: 'Ƴan bindiga sun kashe mutum 49 a kasuwar Goronyo'


Tambuwal

Rahotanni daga jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya na cewa ƴan bidnga sun kashe aƙalla mutum 49 a wata kasuwa a garin Goronyo na jihar.
Wasu ganau sun tabbatar wa da BBC labarin inda suka ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da yamma, yayin da mutanen ke cin babbar kasuwar Goronyon.

Mutanen waɗanda suka buƙaci a sakaya sunayensu saboda tsaro sun ce ƴan bindigar sun afka wa kasuwar ne a yayin da ta cika makil da masu hada-hada daga sassan jihar da ma wasu yankunan.

"Ƴan fashin sun zo ne da misalin ƙarfe 4.30 zuwa biyar na yamma suka zagaye kasuwar suka buɗe wuta ta kowane ɓangare," in ji ganau ɗin.
Majiyarmu ta yi ƙoƙarin jin ta bakin rund8nar ƴan sanda jihar, amma ba mu samu mai magana da yawun ƴan sanda ba a kiran waya da aka yi ta yi masa.

Ya ƙara da cewa "Mutane duk suka ruɗe wasu sun kwakkwanta a ƙasa don gudun harbin ya same su, yayin da wasu suka gudu amma masu tsautsayi sun rasa rayukansu."
Ganau ɗin sun ce an ƙidaya gawa 49 yayin da mutum 17 suka jikkata kuma tuni an kai su asibitin a birnin Sokoto, "gawarwakin kuma an kai mutuwaren da ke babban asibitin garin Goronyo," in ji ɗaya ganau ɗin.

Shaidun sun ce ƴan sandan kwantar da tarzoma da ƴan banga sun yi ƙoƙarin tarwatsa su amma ƴan fashin sun fi su yawa don haka suka kasa shawo kan lamarin.
"Daga baya jami'an tsaro sun je amma lokacin ƴan bindigar sun riga sun tafi," in ji shaidun.

Kowace Goronyo na ci ne a ranar kowace Lahadi, kuma mutane na zuwa daga faɗin jihar Sokoto da wasu jihohin har ma daga Jamhuriyyar Nijar.

Ana yi wa Fulani makiyaya kisan gilla a Sokoto - Miyetti Allah
Ana cikin bala'i a yankin arewa maso yammacin Najeriya — Bafarawa
Abin da ba ku sani ba kan manyan dazukan da ƴan fashi ke ɓuya a Najeriya

Ko a ranar 9 ga watan Oktoban da muke ciki ma akalla mutum 21 aka kashe a harin da ƴan bindiga suka kai a yankin Sabon Birni.
Ƴan bindiga sun buɗe wuta ne a lokacin da mutane ke cin kasuwar garin Unguwar lalle, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC.

Comments

Popular posts from this blog

Musulmai Sun Yi Martani Ga Gumi Bayan Sukar Da Yayi Akan Maulud

Musulman Najeriya sun mamaye shafin Facebook na Dr. Ahmad Gumi. shahararren mai fafutukar kare hakkin ‘yan fashin daji bayan yayi suka ga maulidi a shafin a daidai lokacin da musulman suke  tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad SAWA.  A kowace shekara a cikin watan Rabi’ul Awwal, Musulmin duniya suna tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad ta hanyar karanta Alƙur’ani mai girma, ƙasidun yabo ya Annabi da karanta tarihin rayuwar sa. Shafin Dr. Gumi na Facebook ya samu sharhi sama da 600 har zuwa lokacin nan a tare da cewa suka yayi akan maulidin, amma da yawan su suna rubuta "Happy Maulud,"  duk da sun karanta sukar da yayi.   Karantarwar Dr Gumi tana fuskantar tsaiko da rashin tasiri akan mutane bayan ya karkatar da hankalin sa daga taimakon waɗanda rikicin yan fashin daji ya rutsa da su a arewa maso yammacin Najeriya zuwa neman haƙƙin masu aikata laifin.

PDP za ta 'Kwace mulki daga hannun APC a zaben 2023 - Inji Atiku Abubakar

Alh. Atiku Abubakar Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam'iyyar PDP, Mai adawa, za ta karbi mulki daga hannun jam'iyyar APC, mai mulki, a zaben shekarar 2023. Atku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a dandalin Mahmud Ribadu, Yola, wurin za'ben shugabannin  jam'iyyar PDP na jiha. Ya yi kira ga 'yan siyasa da su mutunta dokokin jam'iyya, na za'be, da Kuma na kundin tsarin mulkin kasar wajen zaben shugabannin jam'iyya, yana mai cewa dimokradiyya na iya 'dorewa ne a cikin yanayi na 'yanci da adalci

'Yan bindiga na karbar dafaffen abinci a matsayin kudin fansa a Jihar Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta dauki wasu tsauraran matakai domin yaki da 'yan bindiga.  Yanzu haka ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna sun bukaci a rika ba su dafaffen abinci a matsayin kudin fansa kafin sakin mutanen da suka yi garkuwa da su. Rahotanni na cewa, ‘yan bindigar sun janye daga kaddamar da hare-hare kan garuruwan jihar tun bayan da gwamnatin ta haramta cin kasuwannin mako-mako a wani bangare na daukar matakin magance matsalar tsaro. Daya daga cikin shugabannin matasan kauyukan Birnin Gwari Babangida Yaro ya shaida wa Jaridar Daily Trsut cewa, tun lokacin da gwamnati ta haramta cin kasuwannin, ‘yan bindigar ke neman a rika ba su dafaffen abinci a duk lokacin da suka sace mutun. Yaro ya kara da cewa, matakin hana sayar da man fetur a yankin, shi ma ya taimaka wajen takaita zirga-zairga. A cewarsa, an samu kwarya-kwaryar zaman lafiya a kauyukan Damari da Kuyello da Kutemashi saboda ‘yan bindigar sun daina kaddamar da farmaki, yayin da suka tare a...