Skip to main content

Harin Goronyo: 'Yadda muka riƙa kutsawa gidajen matan aure don tsira '



Yan bindiga


Ƴan uwa da abokar arziƙin mutanen nan 30 zuwa 60 da suka gamu da ajalinsu yayin wani harin ƴan fashin daji a garin Goronyo da ke jihar Sokoto na ci gaba da jimamin rashin ƴan uwan na su.

Kamar yadda mane labarai suka tattauna da wasu mazauna garin, inda suka bayyana halin da suka shiga, a lokacin da mahran suka yi wa garin kofar rago tare da buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Wani mutum da muka sakaye sunansa, ya ce bai taba ganin tashin hankali a rayuwarsa irin wannan ba, domin ta kai hatta katangar gidan da yake tana jijjiga saboda yadda harbi ya karade gari ko ta ina.

"Ina zaune tare da mutane kawai sai muka ji ana barin wuta, aka ce ai ɓarayi ne, karfe 4:30 na maraice, daga nan kuma muka tashi muka ruga da gudu, muka tsallake katanga muka fada wani gida, ko ina barin wuta ake, ba su tafi ba sai ƙarfe shidda, sannan suka hau baburansu suka wuce.

A cewar wannan mutumin, Allah ne kawai bai sa kwanansa ya ƙare ba, amma ba don haka ba da tuni shi ma yana cikin mutanen da suka mutu.

''Bayan sun tafi ko da na fito sun kashe mutum mutum hudu a bayan gidan da na ɓuya, duka gari dai ya ruɗe kowa yana biɗar ƴan uwansa, abin dai babu daɗin gani ko kadan'' inji wannan shaida, a zantawarsa da tashar BBC

Mutum 20 a dakin matar aure

Taswirar jhar Sokoto

Shi ma wani shaida da muka sakaye sunansa da ke zaune a garin na Goronyo, ya ce kasuwar garin da aka kai harin bata taba cika tun da aka fara damuna kamar ranar da aka kai wannan farmaki da ya janyo mutuwar kimanin mutane 50 ba.

''Ina kusa da asibiti ban ji komai ba sai karar bindiga na tashi, ashe sun kewaye ko ina, da jin haka kuwa sai kowa ya kama gabansa, haka muka yi ta kutsawa gidajen matan aure, sai ka ga muum 20 a dakin matar aure, kuma a gaji a kulle haka nan'' inji shi.

A cewarsa 'an kashe mutum 7 cikin ƴan kato da gorar da suka yi kokarin tunkarar 'yan fashin dajin domin dakile su kafin su far wa jama'ar gari da suke kokarin tunkara.

Abin da Buhari ya ce kan batun

Buhari


Shi dai Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce lokaci na gab da zuwa ƙarshe ga mummunar ɓarnar da 'yan fashin fashin daji ke haddasawa musamman a yankin arewacin ƙasar.

Muhammadu Buhari na wannan jawabi ne a cikin wata sanarwa da ya fitar don juyayin mummunan harin da aka kai kan kasuwar Goronyo wadda ta cika maƙil, inda majiyoyi ke cewa an kashe kimanin mutum 30 zuwa 60 yayin harin na ranar Lahadi.

Ya dai yi kira ga 'yan ƙasar da kada su karaya, maimakon haka su ci gaba da haƙuri don kuwa hukumomi sun duƙufa fiye da kowanne lokaci a baya wajen kare 'yan Najeriya da kuma murƙushe gungun masu ɗauke da makamai.

Comments

Popular posts from this blog

Musulmai Sun Yi Martani Ga Gumi Bayan Sukar Da Yayi Akan Maulud

Musulman Najeriya sun mamaye shafin Facebook na Dr. Ahmad Gumi. shahararren mai fafutukar kare hakkin ‘yan fashin daji bayan yayi suka ga maulidi a shafin a daidai lokacin da musulman suke  tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad SAWA.  A kowace shekara a cikin watan Rabi’ul Awwal, Musulmin duniya suna tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad ta hanyar karanta Alƙur’ani mai girma, ƙasidun yabo ya Annabi da karanta tarihin rayuwar sa. Shafin Dr. Gumi na Facebook ya samu sharhi sama da 600 har zuwa lokacin nan a tare da cewa suka yayi akan maulidin, amma da yawan su suna rubuta "Happy Maulud,"  duk da sun karanta sukar da yayi.   Karantarwar Dr Gumi tana fuskantar tsaiko da rashin tasiri akan mutane bayan ya karkatar da hankalin sa daga taimakon waɗanda rikicin yan fashin daji ya rutsa da su a arewa maso yammacin Najeriya zuwa neman haƙƙin masu aikata laifin.

PDP za ta 'Kwace mulki daga hannun APC a zaben 2023 - Inji Atiku Abubakar

Alh. Atiku Abubakar Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam'iyyar PDP, Mai adawa, za ta karbi mulki daga hannun jam'iyyar APC, mai mulki, a zaben shekarar 2023. Atku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a dandalin Mahmud Ribadu, Yola, wurin za'ben shugabannin  jam'iyyar PDP na jiha. Ya yi kira ga 'yan siyasa da su mutunta dokokin jam'iyya, na za'be, da Kuma na kundin tsarin mulkin kasar wajen zaben shugabannin jam'iyya, yana mai cewa dimokradiyya na iya 'dorewa ne a cikin yanayi na 'yanci da adalci

'Yan bindiga na karbar dafaffen abinci a matsayin kudin fansa a Jihar Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta dauki wasu tsauraran matakai domin yaki da 'yan bindiga.  Yanzu haka ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna sun bukaci a rika ba su dafaffen abinci a matsayin kudin fansa kafin sakin mutanen da suka yi garkuwa da su. Rahotanni na cewa, ‘yan bindigar sun janye daga kaddamar da hare-hare kan garuruwan jihar tun bayan da gwamnatin ta haramta cin kasuwannin mako-mako a wani bangare na daukar matakin magance matsalar tsaro. Daya daga cikin shugabannin matasan kauyukan Birnin Gwari Babangida Yaro ya shaida wa Jaridar Daily Trsut cewa, tun lokacin da gwamnati ta haramta cin kasuwannin, ‘yan bindigar ke neman a rika ba su dafaffen abinci a duk lokacin da suka sace mutun. Yaro ya kara da cewa, matakin hana sayar da man fetur a yankin, shi ma ya taimaka wajen takaita zirga-zairga. A cewarsa, an samu kwarya-kwaryar zaman lafiya a kauyukan Damari da Kuyello da Kutemashi saboda ‘yan bindigar sun daina kaddamar da farmaki, yayin da suka tare a...