Skip to main content

Kotu ta umarci kakakin majalisar Kano da wasu mutane 5 su gurfana a gabanta


Wata babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar Laraba, ta umarci kakakin majalisar jihar Kano da wasu mutane biyar su gurfana a gabanta. 

Wannan umurnin ya biyo bayan wata takarda da aka shigar ta tsohon Shugaban Korafe-korafen Jama'a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa na Jihar Kano, Muhyi Rimin-Gado wanda gwamnatin Kano ta dakatar a watannin baya. 

Sauran wadanda ake kara sun hada da Kwamishinan Shari'a na Kano, Babban Akantan jihar Kano, Kwamishinan 'yan sanda na Kano da Sufeto Janar na' yan sanda. 

Mai shari’a Jane Inyang, wacce ta ba da umarnin, ta nemi su kawo dalili cikin kwanaki biyar da zai sa kotu ba za tayi abinda wanda ya gabatar da ƙara ya nema ba. 

Inyang ta bada umarnin a sanar da wadanda ake kara a cikin kwanaki biyar sannan ta dage karar zuwa ranar 3 ga Nuwamba, don cigaba da sauraron karar. 

Tun da farko, mai gabatar da kara Rimin-Gado a cikin karar ta bakin lauyansa Barista Muhammad Dan’azumi ya gabatar, ya nemi a hana mutane shida da ake kara bincike da sake tsare shi.

Barista Dan’azumi ya kuma roki kotun da ta yi la’akari da abinda mai gabatar da ƙara ya nema, ya kara da cewa wadanda ake kara sun saɓa wa umarnin da babbar kotun Kano ta bayar a baya. 

Idan ba a manta ba, wata babbar kotun Kano karkashin jagorancin Mai Shari’a Sanusi Ado-Ma’aji, a ranar 23 ga Yuli, ta hana Majalisar Dokokin Jihar Kano, Akanta Janar na Jihar Kano da wasu mutum biyu daga ci gaba da binciken Rimin-Gado. 

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito cewa a ranar 5 ga watan Yuli majalisar dokokin Kano ta dakatar da Muhuyi Magaji saboda kin amincewa da akawun da aka kawo masa daga ofishin Babban Akanta na jihar.

Comments

Popular posts from this blog

Musulmai Sun Yi Martani Ga Gumi Bayan Sukar Da Yayi Akan Maulud

Musulman Najeriya sun mamaye shafin Facebook na Dr. Ahmad Gumi. shahararren mai fafutukar kare hakkin ‘yan fashin daji bayan yayi suka ga maulidi a shafin a daidai lokacin da musulman suke  tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad SAWA.  A kowace shekara a cikin watan Rabi’ul Awwal, Musulmin duniya suna tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad ta hanyar karanta Alƙur’ani mai girma, ƙasidun yabo ya Annabi da karanta tarihin rayuwar sa. Shafin Dr. Gumi na Facebook ya samu sharhi sama da 600 har zuwa lokacin nan a tare da cewa suka yayi akan maulidin, amma da yawan su suna rubuta "Happy Maulud,"  duk da sun karanta sukar da yayi.   Karantarwar Dr Gumi tana fuskantar tsaiko da rashin tasiri akan mutane bayan ya karkatar da hankalin sa daga taimakon waɗanda rikicin yan fashin daji ya rutsa da su a arewa maso yammacin Najeriya zuwa neman haƙƙin masu aikata laifin.

PDP za ta 'Kwace mulki daga hannun APC a zaben 2023 - Inji Atiku Abubakar

Alh. Atiku Abubakar Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam'iyyar PDP, Mai adawa, za ta karbi mulki daga hannun jam'iyyar APC, mai mulki, a zaben shekarar 2023. Atku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a dandalin Mahmud Ribadu, Yola, wurin za'ben shugabannin  jam'iyyar PDP na jiha. Ya yi kira ga 'yan siyasa da su mutunta dokokin jam'iyya, na za'be, da Kuma na kundin tsarin mulkin kasar wajen zaben shugabannin jam'iyya, yana mai cewa dimokradiyya na iya 'dorewa ne a cikin yanayi na 'yanci da adalci

'Yan bindiga na karbar dafaffen abinci a matsayin kudin fansa a Jihar Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta dauki wasu tsauraran matakai domin yaki da 'yan bindiga.  Yanzu haka ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna sun bukaci a rika ba su dafaffen abinci a matsayin kudin fansa kafin sakin mutanen da suka yi garkuwa da su. Rahotanni na cewa, ‘yan bindigar sun janye daga kaddamar da hare-hare kan garuruwan jihar tun bayan da gwamnatin ta haramta cin kasuwannin mako-mako a wani bangare na daukar matakin magance matsalar tsaro. Daya daga cikin shugabannin matasan kauyukan Birnin Gwari Babangida Yaro ya shaida wa Jaridar Daily Trsut cewa, tun lokacin da gwamnati ta haramta cin kasuwannin, ‘yan bindigar ke neman a rika ba su dafaffen abinci a duk lokacin da suka sace mutun. Yaro ya kara da cewa, matakin hana sayar da man fetur a yankin, shi ma ya taimaka wajen takaita zirga-zairga. A cewarsa, an samu kwarya-kwaryar zaman lafiya a kauyukan Damari da Kuyello da Kutemashi saboda ‘yan bindigar sun daina kaddamar da farmaki, yayin da suka tare a...