Skip to main content

EFCC ta ƙaddamar da sabon salon yaƙi da rashawa a Najeriya



Shugaban EFCC Abdurrashid Bawa

Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya ce hukumar za ta fifita daƙile aikata laifuka kafin a aikata su
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta ce ta ɓullo da wani sabon salon daƙile ayyukan rashawa, inda za ta fi mayar da hankali kan rigakafin daƙile laifin kafin a aikata shi.

A cewar Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa, daga yanzu hukumar za ta fi mayar da hankali wajen haɗa kai da abokan hulɗarta musamman na ƙasashen waje domin yaƙi da ayyukan rashawa.

Da yake magana yayin taron ƙaddamar da sabon tsarin aikin a Abuja, Abdulrasheed Bawa ya ce sabon tsarin na 2021 zuwa 2025 an ciro shi ne daga kundin muradai na EFCC na shekarar 2013 zuwa 2018.
"Sabon salon ya fi fifita rigakafi (hana faruwar laifi) a matsayin hanya mafi sauƙin daƙile rashawa fiye da yin hukunci," a cewarsa kamar yadda mujallar EFCC ta mako-mako ta ruwaito.

Ya ƙara da cewa sabon tsarin zai fifita tattara bayanan sirri da gurfanar da masu laifi a gaban kotu ta hanyar kyautata tsarin aiki.
A watan Yulin 2021 EFCC ta kaddamar da wata manhaja da za ta bai wa 'yan kasa damar ɗaukar hotunan abubuwa ko wuraren da ake aikata laifuka da zummar aika mata da bayanan.

Manyan jami'an Najeriya shida da suka yanke jiki suka faɗi yayin tuhumarsu
An yanke wa ɗan Abdulrasheed Maina hukuncin ɗaurin shekara 24
Muradi biyar
Kundin EFCC.


Sabon kundin tsarin aikin na EFCC ya ƙunshi muradi biyar
A cewar Abdulrasheed Bawa, sabon salon zai bi tsarin yaƙi da cin hanci na ƙasa wato National Anti-Corruption Strategy (NACS) 2017-2021.

Kazalika akwai muradai biyar da zai mayar da hankali a kan su. Su ne:
Ƙara yawan mu'amala da ɗaiɗaikun jama'a a yaƙi da rashawa
Haɓaka tsarukan yaƙi da rashawa ta hanyar daƙile su kafin su faru
Haɓaka bincike ta hanyar tattara bayanan sirri da gurfanarwa a gaban kotu da ƙwato kuɗaɗen sata
Kyautata tabbatar da doka da kuma haɗa gwiwa da mahukunta
Kyautata aiki da ma'aikatu da kuma ma'aikata abokan hulɗar EFCC
Ma'aikatan EFCC

A matsayinta na hukumar yaƙi da laifukan da suka shafi harkokin kuɗi, EFCC ta ce wannan sabon tsarin aiki zai mayar d hankali kacokam wajen aiki tare da aboka hulɗarta na ƙasashen waje.
Manyan abokan hulɗar sun ƙunshi:
Hukumar Federal Bureau of Investigation ta Amurka
Ƙungiyar Tarayyar Turai
Sashen yaƙi da miyagun ƙwayoyi da laifuka na Majalisar Ɗinkin Duniya, 
Gwamnatin Birtaniya
"Mun nuna hakan ƙarara cikin yunƙurinmu na kyautata alaƙa da dukkan hukumomi wanda ya dace da muradi na huɗu na kundin sabon tsarin," a cewar Bawa.


Comments

Popular posts from this blog

Musulmai Sun Yi Martani Ga Gumi Bayan Sukar Da Yayi Akan Maulud

Musulman Najeriya sun mamaye shafin Facebook na Dr. Ahmad Gumi. shahararren mai fafutukar kare hakkin ‘yan fashin daji bayan yayi suka ga maulidi a shafin a daidai lokacin da musulman suke  tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad SAWA.  A kowace shekara a cikin watan Rabi’ul Awwal, Musulmin duniya suna tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad ta hanyar karanta Alƙur’ani mai girma, ƙasidun yabo ya Annabi da karanta tarihin rayuwar sa. Shafin Dr. Gumi na Facebook ya samu sharhi sama da 600 har zuwa lokacin nan a tare da cewa suka yayi akan maulidin, amma da yawan su suna rubuta "Happy Maulud,"  duk da sun karanta sukar da yayi.   Karantarwar Dr Gumi tana fuskantar tsaiko da rashin tasiri akan mutane bayan ya karkatar da hankalin sa daga taimakon waɗanda rikicin yan fashin daji ya rutsa da su a arewa maso yammacin Najeriya zuwa neman haƙƙin masu aikata laifin.

PDP za ta 'Kwace mulki daga hannun APC a zaben 2023 - Inji Atiku Abubakar

Alh. Atiku Abubakar Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam'iyyar PDP, Mai adawa, za ta karbi mulki daga hannun jam'iyyar APC, mai mulki, a zaben shekarar 2023. Atku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a dandalin Mahmud Ribadu, Yola, wurin za'ben shugabannin  jam'iyyar PDP na jiha. Ya yi kira ga 'yan siyasa da su mutunta dokokin jam'iyya, na za'be, da Kuma na kundin tsarin mulkin kasar wajen zaben shugabannin jam'iyya, yana mai cewa dimokradiyya na iya 'dorewa ne a cikin yanayi na 'yanci da adalci

'Yan bindiga na karbar dafaffen abinci a matsayin kudin fansa a Jihar Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta dauki wasu tsauraran matakai domin yaki da 'yan bindiga.  Yanzu haka ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna sun bukaci a rika ba su dafaffen abinci a matsayin kudin fansa kafin sakin mutanen da suka yi garkuwa da su. Rahotanni na cewa, ‘yan bindigar sun janye daga kaddamar da hare-hare kan garuruwan jihar tun bayan da gwamnatin ta haramta cin kasuwannin mako-mako a wani bangare na daukar matakin magance matsalar tsaro. Daya daga cikin shugabannin matasan kauyukan Birnin Gwari Babangida Yaro ya shaida wa Jaridar Daily Trsut cewa, tun lokacin da gwamnati ta haramta cin kasuwannin, ‘yan bindigar ke neman a rika ba su dafaffen abinci a duk lokacin da suka sace mutun. Yaro ya kara da cewa, matakin hana sayar da man fetur a yankin, shi ma ya taimaka wajen takaita zirga-zairga. A cewarsa, an samu kwarya-kwaryar zaman lafiya a kauyukan Damari da Kuyello da Kutemashi saboda ‘yan bindigar sun daina kaddamar da farmaki, yayin da suka tare a...