Skip to main content

Sauyin dokar zaɓen Najeriya na tayar da ƙura




Shugaban majalisar dattawan Najeriya


Batun sauya dokar zaɓe da gyare-gyaren da majalisar dattawan Najeriya ta yi na ci gaba da haifar da ce-ce-ku-ce a ƙasar.

Bayan jan kafa na wani tsawon lokaci da matsin lamba, majalisar dattawan Najeriya ta ba hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC zaɓin amfani da intanet domin tura sakamakon zaɓe.

Sai dai majalisar dattawan ta ce ba ta yarda da tsarin a aika alƙalumman sakamakon zabe ta intanet ba kaitsaye, sai dai ainahin hoton takardar sakamakon zaben da wakilai suka sanya wa hannu.

A zaman da ta yi na ranar Talata, majalisar dattawan ta ce INEC za ta iya amfani da na'ura ta aika sakamakon zaɓe a lokacin da ya dace idan har hukumar kula da harakokin sadarwa ta Najeriya NCC ta amince.

Majalisar ta kuma kaɗa kuri'ar amincewa da tsarin gudanar da zaɓen fidda ƴan takara na jam'iyyu ta hanyar zaɓe kai tsaye tare da sa idon hukumar INEC.

Majalisar a baya ta ƙi yarda hukumar zaɓen ƙasar ta aika da sakamakon zaɓe ta na'ura, yanzu ta yi gyare-gyaren da a yanzu INEC tana da wuƙa da nama a hannunta na zaɓi tsarin da za ta bi wurin aikewa da sakamakon.

A hirarsa da BBC shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan Najeriyar Sanata Yahaya Abdullahi, ya bayyana cewa sun ɗauki wannan mataki ne saɓanin na da wanda suka yi la'akari da cewa akwai wurare da yankuna na kan iyaka a kusan ko'ina a faɗin ƙasar inda intanet ba ta kai ba, waɗanda kuma a sakamakon hakan za a iya yin maguɗin ƙuri'u.

Majalisar dattawa

Sanatan ya ce bayan wannan ma kuma akwai yuwuwar ƴan ɓata-gari su iya yin kutse su sauya sakamakon zabe.

A bisa la'akari da waɗannan matsaloli ne majalisar a yanzu ta yarda cewa hukumar zaɓe za ta iya amfani da hanyoyi na intanet kamar manhajar WhatsApp da makamantansu ta aika da hoton takardar sakamakon wadda wakilai da sauran masu ruwa da tsaki suka sanya wa hannu, wanda hakan abu ne mai wuya a sauya sakamakon.

Hakan na nufin a yanzu hukumar za ta iya yi wa kanta zaɓin da ta ga ya dace, wato ta aika sakon ko dai ta hanyoyin intanet ko kuma ta hanyar da aka saba bi a baya ta takarda

Sai dai yayin da wasu ƴan ƙasar ke ganin cewa majalisar dattawan ta bayar da kai bori ya hau ne a sakamakon matsi da suka da ta sha, kan ƙin amincewar da ta nuna a baya ga tsarin aikawa da sakamakon ta intanet.

Ɗan majalisar ya ce ko alama ba haka ba ne, sun yi nazari ne kuma suka yi sauyi wanda a yanzu suka amince da wanda suka gabatar.

Me ya rage?

Wannan ana ganin ya zo daidai da bukatun yan Najeriya ne musammam masu korafin cewa rashin bayar da damar ga INEC kamar kwacewa hukumar ne damar da dokokin zabe suka bata.

Masana siyasa a Najeriya kamar Malam Kabiru Sufi, na ganin dama ce yanzu ga hukumar zabe ta yi amfani da zabin guda biyu na aika a rubuce sannan kuma ta aika ta hanyar sadarwa.

Ya ce hanyoyin biyu za su hana yin maguɗi idan aka yi amfani da su. "Idan alkalumman da aka aika a hanyoyin biyu sun yi daidai zai nuna cewa ba a yi magudi ba," in ji shi.

Yanzu abin da ya rage ga waɗannan sauye-sauye da majalisar dattawan ta Najeriya ta yi shi ne kwamitinta na daidaito mai mutane 14 zai zauna ya sake duba dokar zaɓen da kyau kafin a miƙa ta ga Shugaban ƙasar Muhammdu Buhari, wanda zai duba ya kuma sanya mata hannu.

Takaddama a kan soke tsarin zaɓen ƴan takara

Gyaran da majalisar dattawan ta yi, inda ta aiwatar da cewa daga yanzu duk wanda zai tsaya taƙara a kowa ne mataki ƴan jam'iyya ne za su zaɓe shi a fili kai tsaye maimakon tsarin da, wanda wakilai ko daliget (delegates) ke zaɓen ƴan takara, na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce a ƙasar.

Majalisar dattawan a zaman na ranar Talata ta amince cewa daga yanzu duk wanda zai tsaya ko da takarar kansila ko shugaban ƙaramar hukuma ko ɗan majalisar jiha ko sanata ko gwamna ko ma shugaban ƙasa, ƴan jam'iyya masu rijista ne za su yi layi su zabe shi, domin yi wa jam'iyya takara, tsarin da ake kira ƴar-tinƙe ko ƙato bayan ƙato.

Comments

Popular posts from this blog

EFCC ta ƙaddamar da sabon salon yaƙi da rashawa a Najeriya

Shugaban EFCC Abdurrashid  Bawa Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya ce hukumar za ta fifita daƙile aikata laifuka kafin a aikata su Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta ce ta ɓullo da wani sabon salon daƙile ayyukan rashawa, inda za ta fi mayar da hankali kan rigakafin daƙile laifin kafin a aikata shi. A cewar Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa, daga yanzu hukumar za ta fi mayar da hankali wajen haɗa kai da abokan hulɗarta musamman na ƙasashen waje domin yaƙi da ayyukan rashawa. Da yake magana yayin taron ƙaddamar da sabon tsarin aikin a Abuja, Abdulrasheed Bawa ya ce sabon tsarin na 2021 zuwa 2025 an ciro shi ne daga kundin muradai na EFCC na shekarar 2013 zuwa 2018. "Sabon salon ya fi fifita rigakafi (hana faruwar laifi) a matsayin hanya mafi sauƙin daƙile rashawa fiye da yin hukunci," a cewarsa kamar yadda mujallar EFCC ta mako-mako ta ruwaito. Ya ƙara da cewa sabon tsarin zai fifita tattara bayanan sirri da gurfanar da masu laifi a gaban kotu...

Ganduje ya bai wa makaho aiki saboda bajintarsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bai wa Ɗahuru Abdulhamid Idris wanda makaho ne, aikin koyarwa a gwamnatin jihar. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Sakataren Labarai na gwamnatin jihar, Abba Anwar ya fitar a ranar Lahadi. Kafin wannan lokaci, Ɗahuru ya kasance yana aikin koyarwa na sa-kai ba tare da ana biyansa wani albashi ba. Sanarwar ta ce bayan da Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Muhammadu Sanusi Kiru, ya jagoranci Ɗahuru zuwa gaban Ganduje ne, a nan Ganduje ya bada umarnin a ɗauke shi aiki sannan a tura shi Makarantar Nakasassu da ke Tudun Maliki don ya ci gaba koyarwa. Yayin ganawar tasu, Ganduje ya yaba wa ƙoƙarin Ɗahuru musamman ma ganin yadda bai bari lalurar makanta ta hana shi bada tasa gudunmawa ga cigaban fannin ilimin jihar ba. Bisa wannan dalili ne Gwamna Ganduje ya ce, “Lallai ka taki matakin da ya dace a rayuwarka. Gwamnatin jihar Kano ta ba ka aikin koyarwa. Kuma na umarci Kwamishinan Ilimi da a tura ka zu...

PDP za ta 'Kwace mulki daga hannun APC a zaben 2023 - Inji Atiku Abubakar

Alh. Atiku Abubakar Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam'iyyar PDP, Mai adawa, za ta karbi mulki daga hannun jam'iyyar APC, mai mulki, a zaben shekarar 2023. Atku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya kada kuri'arsa a dandalin Mahmud Ribadu, Yola, wurin za'ben shugabannin  jam'iyyar PDP na jiha. Ya yi kira ga 'yan siyasa da su mutunta dokokin jam'iyya, na za'be, da Kuma na kundin tsarin mulkin kasar wajen zaben shugabannin jam'iyya, yana mai cewa dimokradiyya na iya 'dorewa ne a cikin yanayi na 'yanci da adalci