Batun sauya dokar zaɓe da gyare-gyaren da majalisar dattawan Najeriya ta yi na ci gaba da haifar da ce-ce-ku-ce a ƙasar. Bayan jan kafa na wani tsawon lokaci da matsin lamba, majalisar dattawan Najeriya ta ba hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC zaɓin amfani da intanet domin tura sakamakon zaɓe. Sai dai majalisar dattawan ta ce ba ta yarda da tsarin a aika alƙalumman sakamakon zabe ta intanet ba kaitsaye, sai dai ainahin hoton takardar sakamakon zaben da wakilai suka sanya wa hannu. A zaman da ta yi na ranar Talata, majalisar dattawan ta ce INEC za ta iya amfani da na'ura ta aika sakamakon zaɓe a lokacin da ya dace idan har hukumar kula da harakokin sadarwa ta Najeriya NCC ta amince. Majalisar ta kuma kaɗa kuri'ar amincewa da tsarin gudanar da zaɓen fidda ƴan takara na jam'iyyu ta hanyar zaɓe kai tsaye tare da sa idon hukumar INEC. Majalisar a baya ta ƙi yarda hukumar zaɓen ƙasar ta aika da sakamakon zaɓe ta na'ura, yanzu ta yi gyare-gyaren da a yanzu INEC tana da wuƙa ...
Labarai Da-Duminsu